Zamu farfado da Jam’iyar PDP a karamar Hukumar Bichi – Musa Saye
Shugaban Jam’iyyar PDP na karamar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano Alhaji Musa Saye ya ce za su yi aiki sosai domin farfado da martabar jam’iyyar a yankin tare da kare martabarta a dukkan mazabu goma sha daya na karamar hukumar.Alhaji Musa Saye ya yi wannan bayani ne a zantawarsa da ’yan jarida a birnin […]
Shugaban Jam’iyyar PDP na karamar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano Alhaji Musa Saye ya ce za su yi aiki sosai domin farfado da martabar jam’iyyar a yankin tare da kare martabarta a dukkan mazabu goma sha daya na karamar hukumar.
Alhaji Musa Saye ya yi wannan bayani ne a zantawarsa da ’yan jarida a birnin Kano, inda ya bayyana cewa duk da fitar da tsohon dan Majalisar Wakilai na wannan mazaba ta Bichi ya yi, Jam’iyyar PDP tana da magoya baya masu yawa a karamar hukumar wadanda kuma suke da akidar farfado da martabar jam’iyyar.
Alhaji Musa Saye ya kara da cewa tsarin dimokuradiyyar kasar nan ya bai wa kowane dan kasa damar zabar jam’iyyar da zai shiga, don haka babu wata matsala idan wani ko wadansu sun fita daga Jam’iyyar PDP zuwa wata jam’iyya, sannan hakan ko kadan bai karya musu zuciya ba.
Dangane da ayyukan da suke yi na cike gurbin shugabannin da suka koma Jam’iyyar APC kuwa, Alhaji Musa Saye ya bayyana cewa sun bai wa ’yan jam’iyyar na kowace mazaba cikakken iko na zabar shugabannin da suke bukata wadanda kuma za su yi aiki da gaske wajen dawo da martabar jam’iyyar ta PDP a karamar Hukumar Bichi.
Haka kuma shugaban jam’iyyar ya tabbatar da cewa nan gaba kadan, Jam’iyyar PDP za ta zamo abar misali a tsakanin daukacin jam’iyyun siyasa da ake da su a kasar nan musamman ganin cewa jam’iyyar tana cikin zuciyar al’ummar Najeriya a birane da kauyuka, tare da fatan cewa ’ya’yan Jam’iyyar PDP na karamar Hukumar Bichi za su kasance masu jajircewa wajen tafiyar da aikace-aikacen jam’iyya ba tare da nuna kasala ba.
Daga karshe, Alhaji Musa Saye ya yi godiya ga shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar PDP ta kasa, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi da shugaban jam’iyyar na Jihar kano Alhaji Rabi’u dan Sharu da kuma jagoranta a jihar tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau da daukacin mutanen da suke ba jam’iyyar goyon bayan da ake bukata ba tare da nuna gajiyawa ba.