Zan aike wa majalisa ƙudirin ƙarin mafi ƙarancin albashi —Tinubu

Tinubu ya ce zai ci gaba da kare haƙƙin ‘yan Najeriya ta kowace fuska.

Zan aike wa majalisa ƙudirin ƙarin mafi ƙarancin albashi —Tinubu

Shugaba Bola Tinubu, ya ce nan ba da jimawa ba zai aike wa Majalisar Dokoki ƙudiri game da sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata.

Wannan na cikin jawabin da ya yi a yau na bikin cika shekara 25 na tabbatuwar dimokuraɗiyya a Najeriya.

Shugaban, ya ce ya fahimci matsalolin tattalin arziƙi da ƙasar nan ke fuskanta a matsayin al’umma, amma ya buƙaci ’yan Najeriya da su dage don ganin tattalin arziƙi ya inganta.

Alhaji Bukar Goni Aji, ya jagoranci kwamitin mutum 33 kan mafi ƙarancin albashi na ƙasa a ranar Litinin, inda ya gabatar da rahotonsa bayan shafe kusan watanni biyar yana zama.

Wakilan gwamnatin tarayya da kamfanoni masu zaman kansu sun buƙaci Naira 62,000 ya zama mafi ƙarancin albashi, yayin da ƙungiyoyin ƙwadago suka rage buƙatarsu daga Naira 494,000 zuwa Naira 250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata.

Bayan gabatar da rahoton, ana sa ran shugaban zai yanke shawara tare da aike da ƙuduri ga majalisar dokoki don zartar da mafi ƙarancin albashi, wanda shugaban zai sanya hannu ya zama doka.

Yayin da yake jawabi a yau, shugaba Tinubu ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta ƙaddamar sun zama dole ne duba da halin da tattalin arziƙin ƙasar nan ke ciki.

“Tattalin arziƙinmu ya jima yana son gyara. Babu abin da ke tafiya daidai, ƙasar nan ta dogara da samun kuɗin ta hanyar man fetur.

“Sauye-sauyen da aka yi na da nufin ƙarfafa tattalin arziƙi da kuma samar da makoma mai kyau. Babu kokwanto sauye-sauyen sun jefa jama’a cikin matsi amma sun zama dole ne a aiwatar da su don samar da tattalin arziƙi mai ƙarfi ga kowa. Yayin da muke farfaɗo da tattalin arziƙi zan ci gaba da sauraron jama’a kuma ba zan taɓa juya muku baya ba”, in ji Tinubu.

Shugaba Tinubu ya buƙaci a kare dimokuraɗiyyar Najeriya ta kowane hali, inda ya jadadda cewar zai ƙoƙari wajen kare haƙƙin ’yan Najeriya.