Zan amince da sakamakon zabe da zuciya daya – Tambuwal
Bayan kada kuri’arsa Gwamnan Sakkwato kuma Dan takarar Gwamna a jam’iyar PDP Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya yi alkawarin karbar sakamakon zabe da zuciya daya. Ya bayyana fitowar jama’a don kada kuri’arsu musamman mata abin yabawa ne. Tambuwal ya yi wadan nan kalamai ne ga manema labarai a zantawarsa da su a garin Tambuwal.”Abin da […]
Bayan kada kuri’arsa Gwamnan Sakkwato kuma Dan takarar Gwamna a jam’iyar PDP Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya yi alkawarin karbar sakamakon zabe da zuciya daya.
Ya bayyana fitowar jama’a don kada kuri’arsu musamman mata abin yabawa ne.
Tambuwal ya yi wadan nan kalamai ne ga manema labarai a zantawarsa da su a garin Tambuwal.”Abin da nake gani zaben nan ya gudana cikin lumana da kwanciyar hankali duk da akwai ‘yan kalubale nan da can kadan. Babu wata rigima ko hargitsi dana samu labari”.
Tambuwal ya kada kuri’arsa da misalin karfe 12:25 na rana, ya yi kira da jama’a su zauna lafiya da junansu Allah ya riga ya zabi wanda zai jagoranci jama’a.