Zan ba Buhari kyautar jakina a Abuja -Murtala Sintau

Aminiya ta samu tattaunawa da Malam Murtala Muhammadu Sintau, wanda ya hawo jaki tun daga Zamfara zai je Abuja domin halartar bikin rantsar da zababben shugaban kasa Muhammadu Buhari, a yayin da yada da zango a Zariya. Aminiya: za mu so ka gabatar da kanka da kuma dalilin wannan tafiya a kan jaki?Sunana Murtala Muhammadu […]

Zan ba Buhari kyautar jakina a Abuja -Murtala Sintau

Aminiya ta samu tattaunawa da Malam Murtala Muhammadu Sintau, wanda ya hawo jaki tun daga Zamfara zai je Abuja domin halartar bikin rantsar da zababben shugaban kasa Muhammadu Buhari, a yayin da yada da zango a Zariya.

Aminiya: za mu so ka gabatar da kanka da kuma dalilin wannan tafiya a kan jaki?
Sunana Murtala Muhammadu Sintau, na fito daga dan’ali da ke karamar hukumar Birnin Magaji a jihar Zamfara, kuma shekaru na talatin, inada mata biyu, amma ba ni da da, sai dai na baro matana duka da ciki, kuma sana’ata noma da saida katin waya kuma ina taba siyasa. shi kuma wannan jakin da kake gani tare muke yawon kamfen da shi tun a wancan siyasar da ta wuce ta 2015. Tun a wancan lokaci Allah Ya sa mun soyayyar Buhari a zuciyata, har mutane suna daukana a matsayin mahaukaci, duk inda na wuce sai a dunga tsokanata, ganin mun fadi zabe a wancan lokacin sai wahalar banza nake, ko wannan karon ma ba za mu ci zabe ba, haka abokan adawa suke ce mana, har sai da na yi hijira kafin zuwan wannan lokaci da Allah Yakunyata su muka ci zabe.
Don haka ni ma kamar kowane dan Nigeriya zan halarci bikin rantsarwa tare da jakina domin mu nuna farin cikinmu ni da wannan jakin, wannnan shi ne dalilina na zuwa Abuja. Kuma kafin in fito gida sai da na sanar da iyayena da kuma matana tare da limamin garinmu da kuma shugaban jam’iyarmu, duk suka yi min fatan alheri.
Aminiya: Wane kalubale ka fuskanta a tafiyarka?
kalubalen da na fuskanta ba shi da yawa, illa a masarautar Gusau da na isa na ce ina son in ga Sarki, bayan an karbi takarduna sai Shamaki ya ce bazan ganshi ba, wannan shi kadai ne ya bata mini rai a tafiyata
Aminiya: Wane nasarori ka samu a kan hanya?
A gaskiya na samu nasarori da dama a kan hanya ta kwana biyar da na dauka daga Zamfara zuwa nan garin Zariya, duk inda na taho sai ka ga mutane sun fito suna karbata, kamar yadda ka gani a nan, suna mini fatan alheri. Sai dai a garin Funtuwa lamarin ya sha bamban, domin sun karrama ni fiye da inda ake zato, don har rako ni suka yi bakin iyaka. Kuma a gaskiya na fito da isasshen guzirina tare da na jakina, domin na fito da buhun harawar gyada biyu tare da dawar da zan rika ba shi har mu kai, kuma duk inda na tarar da marmara sai in sauka in rika kora shi, har mu wuce marmarar. Kuma isha Allah za mu isa Abuja kafin kwanakin da ya rage a rantsar da jagorar talakawa, kuma idan na isa shi wannan jakin Buhari zan bar masa shi kyauta, domin shi ma mutumin karkara ne, don ya zama masa matashiya ne a kanmu.