Zan canja fasalin Najeriya idan na zama Shugaban Kasa- Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya ce idan ya zama shugaban kasa a zaben 2019, zai canja fasalin Najeriya a cikin wata shidan farko na mulkinsa. Atiku Abubakar ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake amsa tambayoyi a Chatham House na Landan, bayan ya kaddamar da makala mai taken: Muhimmancin karfafa tattalin […]

Zan canja fasalin Najeriya idan na zama Shugaban Kasa- Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya ce idan ya zama shugaban kasa a zaben 2019, zai canja fasalin Najeriya a cikin wata shidan farko na mulkinsa.

Atiku Abubakar ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake amsa tambayoyi a Chatham House na Landan, bayan ya kaddamar da makala mai taken: Muhimmancin karfafa tattalin arziki da yanayin lura da bangaren.

Hakanan kuma Atiku ya ce bai ba dukan jihohin Najeriya 36 tallafin kudi na Dala miliyan 250  domin su sama damar fadada hanyoyin samun kudin shiga.

Ya kuma ce bai yi mamaki ba don Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce matasan Najeriya ragwaye ne, domin a cewarsa, shi Buharin bai taba jagorantar wani kasuwanci ba.

“Abin da nake fada wa yawancin ‘yan Najeriya shi ne idan na yi wata shida, zan yi iya canja fasalin kasar cikin sauri. Wannan abu ne mai sauki domin babu jihar da za ka kira ka ce mata za ka xora mata wani nauyi da kuma arzikinta ta ce maka a’a.”