Zan canja rayuwar matan Bauchi idan aka zabe ni Gwamna –Maryam APC
daya daga cikin masu fafutikar neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar APC Hajiya Maryam Muhammed wadda aka fi sani da Maryam APC ta bayyana cewa a shirye take ta inganta rayuwar mata da matasan jihar da ke fama da matsaloli sakamakon rashin shugabanci nagari.Hajiya Maryam ta bayyana haka ne lokacin da take […]
daya daga cikin masu fafutikar neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar APC Hajiya Maryam Muhammed wadda aka fi sani da Maryam APC ta bayyana cewa a shirye take ta inganta rayuwar mata da matasan jihar da ke fama da matsaloli sakamakon rashin shugabanci nagari.
Hajiya Maryam ta bayyana haka ne lokacin da take tattaunawa da wakilinmu a Bauchi, inda ta kara da cewa a matsayinta na ’yar siyasa za ta cigaba da wayar mata da matasa ta yadda za su kada mata kuri’a a zaben shekara ta 2015 da muke tunkara.
To sai dai kuma daga bisani ta karyata masu yada jita-jitar cewa wai wasu daga cikin ’yan PDP ne suka tura Jam’iyyar APC domin jawo rudani a lokacin zaben fidda-gwani na jam’iyyar da za a gudanar nan da wasu watanni.
Ta ce tunda ta fara siyasa ba ta taba shiga jam’iyyar PDP ba kuma za ta ci gaba da zama a jam’iyyar adawa har zuwa lokacin da za a samu shugabanni masu gaskiya da rikon amana da suke shirye su inganta rayuwar al’ummar Jihar Bauchi.
Hajiya Maryam ta bukaci shugabannin Jam’iyyar APC su yi adalci ga duk wani dan takara domin da yawa daga cikin ’yan Najeriya sun zuba ido suna kallon Jam’iyyar APC.