Zan ceto rayuwar matasan Jihar Bauchi – Barista Jibirin

Wani fitaccen lauya mai zaman kansa da ke son tsayawa takarar Majalisar Tarayya daga mazabar karamar Hukumar Bauchi a karkashin Jam’iyyar APC, Barista Jibrin S. Jibrin ya nuna damuwa bisa yadda ake ci gaba da samun dimbin matasa da ke zaman kashe wando a karamar hukumar.  Barista Jibirin ya ce Allah Ya albarkaci karamar hukumar […]

Zan ceto rayuwar matasan Jihar Bauchi – Barista Jibirin
Zan ceto rayuwar matasan Jihar Bauchi – Barista Jibirin

Wani fitaccen lauya mai zaman kansa da ke son tsayawa takarar Majalisar Tarayya daga mazabar karamar Hukumar Bauchi a karkashin Jam’iyyar APC, Barista Jibrin S. Jibrin ya nuna damuwa bisa yadda ake ci gaba da samun dimbin matasa da ke zaman kashe wando a karamar hukumar. 

Barista Jibirin ya ce Allah Ya albarkaci karamar hukumar da dimbin matasa amma da yawa suna fama da rashin aiki. “Sakamakon binciken da muka gudanar kwanaki mun gano kashi 85 cikin 100 na matasan karamar hukumar ba su da aiki sai shan miyagun kwayoyi da zaman kashe wando.
Barista Jibrin ya bayyana haka ne a zantawa da wakilin Aminiya a karshen makon jiya. Baristan ya ce ya fito takara ne domin ceto rayuwar matasan domin matukar aka samar wa matasa abin yi za a samu raguwar aikata laifuffuka a tsakanin al’umma.
A cewarsa PDP za ta dandana kudarsu a zaben shekarar 2015 domin ta gaza kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya daga1999 zuwa yau. Daga karshe ya yi kira ga matasa su guji masu amfani da su a lokacin zabe don tada zaune-tsaye.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi