Zan cika dukkan alkawuran da na dauka – Shugaba Buhari
A ranar Talatar da ta gabata ne Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi na Naira tiriliyan takwas da biliyan 600, kimanin Dala miliyan dubu 28 a gaban majalisun dokokin kasar mai cike da kudiri na farfado da tattalin arzikin Najeriya a shekarar 2018. A lokacin da shugaban ke gabatar da wannan kasafi […]

A ranar Talatar da ta gabata ne Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi na Naira tiriliyan takwas da biliyan 600, kimanin Dala miliyan dubu 28 a gaban majalisun dokokin kasar mai cike da kudiri na farfado da tattalin arzikin Najeriya a shekarar 2018.
A lokacin da shugaban ke gabatar da wannan kasafi a gaban zaman hadin gwiwa na majalisun dokokin, ya ce wannan kari ne na kashi 16 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2017, hakan kuma zai taimaka wajen cika muradun gwamnati na farko wato a fannoni na tattalin arziki da suka hada da samar da hanyoyi da kula da fannin lafiya da samar da gidaje da ayyukan yi.
Za a dora hasashen samun kudaden tafiyar da kasafin kan fitar da gangar danyan mai miliyan dubu biyu da digo uku a kowace rana, sabanin miliyan dubu biyu da digo biyu a shekarar da ta gabata, inda za a sayar da kowace ganga akan Dala 45 sannan bisa cnajin dalar Amurka 305.
A jawabinsa ga majalisar dokin kasar yayin gabatar da kasafin, inda ya shafe kimanin sa’a daya da rabi yana bayani. Shugaba Buhari ya ce burin gwamnatinsa shi ne cika alkawura da suka yi wa ‘yan Najeriya a lokacin yakin neman zabe kana kuma gwamantin tasa tana son samar wa talakawa ababan more rayuwa.
Ya kara da cewa gwamnati za ta kashe naira biliyan 300 kan gyara hanyoyi a fadin Najeriya. Haka kuma za ta ware naira biliyan 8.9 domin tashar samar da wutar lantarki ta Mabila.
Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta samu ta yi hanyoyin kwalta na sama da kilomita 766 a fadin kasar nan a kasafin kudin shekarar 2017. Wannan ne dai kasafin kudi na biyu da shugaban kasar ya gabatar ga majalisun dokokin tun bayan da ya hau karagar mulki a shekarar 2015.
Shugaban ya ce ba ya ga inganta harkokin noma da samar da makamashi, gwamnatinsa ta mayar da hankali ne kan biyan basussukan ayyukan da gwamnatocin baya suka bari ga ‘yan kwangila domin a kammala ayyukan samar da ababen more rayuwa a kasar. Sai kuma ya bukaci al’ummar Najeriya da su kwana da tabbacin cewa gwamnatinsa tana iya abin da za ta iya yi domin samar da dauwamammiyar wutar lantarki a fadin kasar baki daya.
Haka zalika Shugaba Buhari ya soke damar daukar sabbin ma’aikata da dukkanin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da ita a baya, har sai sun samu amincewar ofishinsa kai tsaye.
A cewar shugaban matakin zai saukakawa gwamnati wajen kyautata amfani da kudade a kan ka’ida wajen tafiyar da ayyuka da albashi ba tare da samun gibi ba. Hakan kuma zai kara taimakawa, wajen bin ka’idojin da suka kamata yayin daukar sabbin ma’aikata.
Yayin da yake karin haske kan halin da ake cikin dangane da aiwatar da kasafin kudin wannan shekara, shugaba Buhari ya ce zuwa karshen watan Oktoba, gwamnatinsa ta fitar da naira biliyan 450, daga cikin tiriliyan 2.2, da aka ware domin gudanar da manyan ayyuka a kasar.
A cewarsa zuwa karshen watan Disamba mai zuwa gwamnatinsa za ta cimma burin aiwatar da kashi 50 na kasafin kudin shekarar 2017. Koda yake ya dora alhakin tsaikon da aka samu wajen aiwatar da kaso mafi yawa na kasafin kudin na 2017 bisa rashin amincewa da kasafin a kan lokaci da ‘yan majalisun suka yi, wanda ya jawo rashin fitar da kudaden da ake bukata akan lokaci. Naira tiriliyan 3.5 daga cikin kasafin na tiriliyan 8.6, za su tafi ne wajen gudanar da ayyuka na yau da kullum, yayin da aka warewa manyan ayyuka naira triliyan 2.7.
A bangaren biyan wani yanki na bashin da ake bin Najeriya kuwa, Shugaba Buhari ya ce za a yi amfani da naira tiriliyan 2. Dangane da farashin gangar danyen mai da aka kafa turakun kasafin kudin kuwa, shugaban ya ce an dora shi ne bisa dala 45 kan kowacce gangar danyen man, sabanin dala 44 kan kowace ganga da aka gina kasafin kudin shekarar 2017.