‘Zan dauki mataki a kan…’

Saboda haka ba za ka ce don na fito na ce ga barna a cikin ’yan sanda cewa na wulakanta aikin ba. Wanda kuma duk ka ji ya ce haka, to irin mutanen nan ne da ba su son gyara. Sannan kada ka manta barna tana da sauki, amma ita gyara sai an wahala, rashawar […]

‘Zan dauki mataki a kan…’

Saboda haka ba za ka ce don na fito na ce ga barna a cikin ’yan sanda cewa na wulakanta aikin ba. Wanda kuma duk ka ji ya ce haka, to irin mutanen nan ne da ba su son gyara. Sannan kada ka manta barna tana da sauki, amma ita gyara sai an wahala, rashawar nan wadansu da yawa na jin dadinta, wadansu sun gina aljannnar duniya da ita. Wannan ya sanya kake ganin irin wadannan zantukan barkatai.

Bayan wanke ka, shin akwai matakin da kake shirin dauka?

To ina nan ina dubawa tukuna, domin ba lamari ne da ya shafe ni a karan kaina ba, lamari ne da ya shafi Majalisar Dattawa baki daya, domin na yi wannan bincike ne a matsayina na dan majalisa. Dole sai mun yi magana da su sannan mu ga matakin da ya kamata mu dauka! Shin abu ne da za a iya yin shiru ko za a nemi hakki a kai? Duk wadannan abubuwa za mu duba su nan gaba kadan.

Wannan yaki za a iya cewa da Shugaban ’Yan sandan Najeriya kake yi kai-tsaye a kan rashawa. Shin me kake so a yi?

Abubuwan da muke so suna da yawa, akwai matsaloli masu yawa game da yadda ake tura wa rundunar ’yan sandan kudaden ayyukan da suke tura jami’ai rin su kamfanoni, bankuna da sauransu. To wadannan kudade maimakon su rika zarcewa aljihun mutune, muka ce ya kamata su rika shiga aljihun gwamnati, ka ga idan akwai wannan, to gwamanti za ta iya sake dawo wa ’yan sanda wadannan kudi da su za a ba su horo, da su za a yi bariki, sannan a sayi motocin aiki da sauransu. Dubi motocin ’yan sanda a yau! Ka ga za a samu canji da sauki, hatta matsalolin rashin albashi da suka addabi rundunar za a magance su. To wannan shi ne abin da muke so.