Zan dauki mataki kan Rundunar ’Yan sanda idan… – Sanata Misau

Sanata Isah Hamma Misau, Sanatan Bauchi ta Tsakiya, wanda Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta zarge shi da gudu daga aiki ya shaida wa Aminiya, jim kadan bayan da Hukumar Ayyukan ’Yan sanda ta tabbatar da sahihancin ajiye aikinsa, cewa borin kunya rundunar ta yi don dauke hankalin ’yan Najeriya daga zargin da ake yi mata. […]

Zan dauki mataki kan Rundunar ’Yan sanda idan… – Sanata Misau

Sanata Isah Hamma Misau, Sanatan Bauchi ta Tsakiya, wanda Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta zarge shi da gudu daga aiki ya shaida wa Aminiya, jim kadan bayan da Hukumar Ayyukan ’Yan sanda ta tabbatar da sahihancin ajiye aikinsa, cewa borin kunya rundunar ta yi don dauke hankalin ’yan Najeriya daga zargin da ake yi mata. Kuma ya ce za su ci gaba da taya Shugaba Buhari yaki da rashawa ba gudu ba ja da baya. Ga yadda takaitacciyar tattaunawar ta kasance: 

 

Yallabai, a ’yan kwanakin nan hankalin ’yan Najeriya ya koma kan dambarwar dake tsakaninka da Rundunar ’Yan sandan Najeriya game da batun ritayarka daga aiki, kwatsam sai Hukumar Ayyukan ’Yan sanda ta wanke ka, yaya ka ji?

Gaskiya na yi wa Allah godiya bisa bayyanar gaskiya cikin kankanen lokaci. Tun farko rundunar ta so ne ta shashantar da zarge-zargen da muka gabatar a kanta. Batun cewa suna nemana ruwa a jallo ko ban ajiye aikin dan sanda bisa ka’ida ba da sauransu duk kame-kame ne kawai. Don haka tunda suka fara wannan kame-kamen na san cewa ba damuwata ba ce damuwarsu ce. 

Wannan aiki fa na shafe fiye da shekara 10 cikinsa, na san dokokin aikin ciki da waje sannan na sadaukar da kaina, kuma saboda yadda na sadaukar da kaina a aikin dan sanda ko hutun shekara-shekara da ake yi, ban taba zuwa ba. Sannan bayan duk wannan gwagwarmaya wani ya fito rana tsaka ya ce wai ban ajiye aiki kan ka’ida ba. To tun farko gaskiya ba damuwata ba ce, domin dokar Najeriya ta shimfida ka’idojin barin aiki da suka hada da ba da wa’adin wata uku ko biyan albashin wata guda, to duk an yi wannan. Amma domin sharri sai rundunar ta dauko wani sabon salo don dauke hankulan jama’a kada a fahimci asalin abin da ake magana a kansa. Ban san aikin ba ne tsawon wadannan shekarun? Sannan haka kawai ina aikin dan sanda zan je in shiga siyasa? Ai hankali ma ba zai dauki wannan ba. Sannan ina da abokan hamayya, ko su suka san cewa ban ajiye aikin dan sanda bisa ka’ida ba, ai da tuni sun shigar da kara a kotu. Ba ma a shekarar 2015 ba, hatta a shekarar 2011 a Jam’iyyar CPC, lokacin mun yi zazzafar takara kuma na kada mutane da yawa wadanda kwarrun ’yan siyasa ne.

Ba na jin mutum irina zai yi wannan kuskuren. Wannan duk suna yi ne don karya min gwiwa, kuma ina tabbatar maka cewa wannan ba zai karya gwiwa ba, za mu ci gaba da aiki don taimaka wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yaki da cin hanci da rashawa. Duk inda muka ga ana yin ba daidai ba za mu yi magana. Sannan na fadi tun lokacin cewa wannan kora-kunya da hauka ce ’yan sanda ke yi, kuma ga shi ya tabbata haka ne. Hukumar Ayyukan ’Yan sanda ta ce ita ta ba da wannan takarda ta barin aikina daga aikin dan sanda, ka ga wannan yana nuna cewa wasan kwakwayon ya yi kusan karewa, yanzu ko suna so ko ba su so, dole su dawo kan wancan magana da muka fada a kansu, su fito su gaya wa duniya gaskiyar lamari. 

Ba ka ganin kamar za a ce kila kamun kafa ka yi a hukumar ta wanke ka? 

Ai duk wanda ya san ni, ya san ba haka nake ba, kuma abu na biyu wannan fa hukuma ce mai karfin gaske, kuma ina tabbatar maka cewa ban taba zuwa hukumar ba sam. Kuma ko lokacin da hukumar ta kira ni na gaya mata cewa ba ta da hurumin kira na, saboda ba neman aiki nake yi wajenta ba, kuma ni ba ma’aikacin wajen ba ne, wanda za su iya kira kawai shi ne ma’aikacinsu ko wanda ke aikin dan ’yan sanda ko wanda ke neman aiki a wurin, to shi ne za a ce masa ya zo da kwafen takardarsa a gani, hukumar nan fa ita ta ba ni wannan takarda, kuma wanda yake hannuna nawa ne, na ta kuma na can wajenta. 

Sanata ka gaji aikin dan sanda, kai ma ka yi aikin. Ba ka ganin wadansu za su ce ka wulakanta aikin ne kan bankado almundahanar da ka yi?

Ka san kowa da irin fahimtarsa, misali lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya binciki ofishin Mai Ba da Shawara kan Tsaro (NSA) har aka kama Sambo Dasuki, ya wulakanta ofishin ne? Ko da aka kama shugabannin sojoji su Aled Badeh, ya wulakanta aikin ne? Ai shi ma tsohon soja ne, rashin gaskiya rashin gaskiya ce! Kuma gyara ya fi alheri, idan ka bar rashin gaskiya ya ci gaba da faruwa musamman a irin wannan waje na tsaro, to zai iya illar da za ta shafi al’ummar Najeriya kusan miliyan 200 a nan gaba.