Zan dawo da aikin yashe Kogin Neja muddin aka zabe ni – Tinubu
Ya yi alkawarin ne yayin kamfen dinsa a Minna
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin dawo da aikin yashe Kogin Neja da aka yi watsi da shi, muddin aka zabe shi a 2023.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Kwamitin Yada Labaran tsohon Gwamnan na Jihar Legas ya karyata labarin da ake yadawa cewa an garzaya da maigidan nasa asibiti ana tsaka da kamfen.
- Kotun Kano ta yanke wa dan Hisbah hukuncin kisa ta hanyar rataya
- Malam bude mana littafi: Kwaron da ke bad-da kama ya yi kama da maciji
Tinubu dai ya yi alkawarin ne ranar Laraba a Minna, babban birnin Jihar Neja, jim kadan bayan kammala wata tattaunawarsa da manoma da masu sayar da kayan amfanin gona a Jihar.
Dan takarar ya kuma ce, “Jiharku na da dimbin albarkatu masu tarin yawa. Ba wai kawai ita ce Jihar da ta fi kowacce fadi ba a Najeriya, ita ce kuma take da manyan tashoshin lantarkin da ke haskaka kasar nan.
“Da yardar Allah, zan ci zabe, kuma idan haka ta tabbata, gwamnatina za ta taimaka wajen habaka albarkatun wannan Jihar. Muna alfahari da gudunmawarku a matsayinku na mai samar wa Najeriya wutar lantarki. Wannan Jihar za ta fi haka karfi a nan gaba kadan,” inji Tinubu.
Gangamin dai ya samu halartar Mataimakin takarar Tinubu, Sanata Kashim Shettima da Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan da Shugaban APC na Kasa, Abdullahi Adamu da kuma dan takarar Gwamna na jam’iyyar a Jihar, Mohammed Umar Bago, da dai sauransu.
Kafin ya koma Abuja dai, Tinubu ya kai ziyara ga Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago, sannan ya kaddamar da ofisoshin yakin neman zaben Sanata Sani Musa Mohammed da Alhaji Mohammed Idris.