Zan dawo da wadanda suka yi hijira daga masarautata – Sarkin Wase

Mai martaba Sarkin Wase da ke Jihar Filato Alhaji Sambo Haruna Muhammadu ya yi alkawarin cewa zai dawo da duk mutanen da suka yi gudun hijira daga masarautarsa, zuwa wasu wurare sakamakon rikice-rikicen da aka yi a masarautar daga 1998 zuwa shekara ta 2010. Sarkin ya yi wannan alkawari ne a lokacin da yake jawabi […]

Zan dawo da wadanda suka yi hijira daga masarautata – Sarkin Wase
Zan dawo da wadanda suka yi hijira daga masarautata – Sarkin Wase

Mai martaba Sarkin Wase da ke Jihar Filato Alhaji Sambo Haruna Muhammadu ya yi alkawarin cewa zai dawo da duk mutanen da suka yi gudun hijira daga masarautarsa, zuwa wasu wurare sakamakon rikice-rikicen da aka yi a masarautar daga 1998 zuwa shekara ta 2010.

Sarkin ya yi wannan alkawari ne a lokacin da yake jawabi ga tawagar yakin neman zaben Gwamnan Jihar Filato karkashin Jam’iyyar APC ta kai masa gaisuwa a fadarsa da ke garin Wase.
Sarkin ya ce a rikice-rikice wadanda wasu ’yan siyasa masu son kansu suka hada a masarauta an kone kauyuka sama da100. Ya ce “A matsayina na uba a wannan masarauta zan hada kan al’ummar masarautar domin mu zamo daya ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba.”
Sarkin ya yi kira ga ’yan siyasar Najeriya kan su hada kan al’ummar Najeriya kuma su rika sanya kishin kasa a yakin neman zaben da suke yi a halin yanzu.
Tun da farko a jawabin dan takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar APC, Mista Simon Lalong ya ce sun ziyarci Sarkin na Wase ne domin neman goyon bayan fadar Sarkin. Ya ce muna rokon goyon baya kuma muna rokon a yi mana addu’a kan wannan takara da muke yi.