Zan dawo don shirin sake zama Gwamnan Jihar Adamawa – Nyako

Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Admiral Murtala Nyako ya bayyana cewa kwanan nan zai koma jiharsa ta Adamawa domin fara shirye-shiryen gudanar da yakin neman zabe don ganin ya yi nasarar sake zama Gwamnan Jihar a shekarar 2019. Admiral Murtala Nyako, ya bayyana haka ne a lokacin da wata tarba da jama’arsa suka yi masa a […]

Zan dawo don shirin sake zama Gwamnan Jihar Adamawa – Nyako


Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Admiral Murtala Nyako ya bayyana cewa kwanan nan zai koma jiharsa ta Adamawa domin fara shirye-shiryen gudanar da yakin neman zabe don ganin ya yi nasarar sake zama Gwamnan Jihar a shekarar 2019.

Admiral Murtala Nyako, ya bayyana haka ne a lokacin da wata tarba da jama’arsa suka yi masa a filin saukar jiragen sama, don yi masa ta’aziyyar rashin tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Alhaji Saleh Michika wanda ya rasu a Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Yola kawanakin baya.

Tsohon Gwamnan ya gargadi Jam’iyyar APC cewa ta yi hattara wajen tsayar da ’yan takararta tare da kauce wa tsayar da wadanda ke kan kujera a jam’iyyar ba tare da bin ka’idoji da kuma yadda dokar kasar ta tsara ba. 

Ya kara da cewa idan APC ta kasance mai bai wa kowa damar rike kujera ba tare da bin ka’ida ba, to lallai kowane kare da doki ma zai iya yin mulki a jihar.

Nyako ya ce jam’iyyar za ta iya fuskantar rikici idan har ba a gudanar da abubuwa bisa yadda doka ta tsara ba, domin siyasa ba abar wasa ba ce kuma ya kamata a bi ka’ida domin abu ne da ya shafi hakkin jama’ar jihar da kasar baki daya.

“Adalci wajen gudanar da harkokin siyasa shi ne mabudin ci gaban jam’iyya a kasar nan, amma idan aka sanya rashin adalci da rashin bin doka, akwai alamar tarwatsewar jam’iyyar,” inji shi. Sai ya yi kira ga masoyansa da su yi amfani da damar da suke da ita wajen zabar shugabanni nagari wadanda suka ga sun dace da su a lokacin zaben shekarar 2019 mai zuwa.