Zan dora daga inda Kwankwaso ya tsaya – Ganduje
Zababben Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Gauduje ya ce zai ci gaba dorawa daga inda Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ya tsaya domin ci gaban jihar, domin samun nasara a kowace Gwamnati ya dogara ne ga ci gaba da aikin da wanda ya gabata ya tsaya. Dokta Abdullahi Ganduje ya bayyana haka ne a Yola […]
Zababben Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Gauduje ya ce zai ci gaba dorawa daga inda Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ya tsaya domin ci gaban jihar, domin samun nasara a kowace Gwamnati ya dogara ne ga ci gaba da aikin da wanda ya gabata ya tsaya.
Dokta Abdullahi Ganduje ya bayyana haka ne a Yola lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai, ya ce abin takaici shi ne Gwamnatoci da dama a jihohin kasar nan suna kasa samun nasara ne saboda ba su ci gaba da dorawa daga inda wanda ya bar mulki ya tsaya.
Ya ce Gwamnatinsa ba za ta bar kan hanyar da Gwamna Kwankwaso ya tsara ba, kuma in akwai ayyukan da ba a gama su ba, zai ci gaba har ya kammala su. “Kodayake na kasance a cikin Gwamnatin Kwankwaso kuma na riga na san ayyukan da ya kamata a ci gaba. Zan yi iya kokarina in ga cewa an gama wadancan ayyuka domin samun ci gaba a jihata kafin na fara yin wasu sababbin ayyuka,” inji shi.
Zababben Gwamna ya ce matsalolin kasuwanci da aka samu a kasar nan zai iya iya kokarinsa domin ya ga jiharsa ta samu nasara da riba a wajen tafiyar da harkar kasuwanci. Ya ce wadanda harkar kasuwancinsu ba mai yawa ba ne ba za a takurasu ba wajen biyan haraji.
Game da cin hanci da rashawa, Dokta Ganduje ya ce Gwamnatinsa ba za ta saurara wa wadanda aka kama da irin wannan hali a jiharsa ba.
Ya sake ba da shawara ga zababben Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ya yi bincike a kan wadanda suka yi almubazzaranci da kudin Gwamnati domin samun gyara a Gwamnatinsa.