Zan fada da Hausa!

Wani Babarbare ne direban babbar mota ya dauki gyada zai kai wani wuri, sai ya zo shingen sojoji, suka tsaida shi ya yi masa Ingilish ‘weting  for  inside’ wato mene ne a ciki?  Babarbare bai jin Ingilish, amma wai dole ya yi, sai ya ce  Oga  gurnet  ne (yana nufin groundnot wato gyada). Aka ce […]

Zan fada da Hausa!
Zan fada da Hausa!

Wani Babarbare ne direban babbar mota ya dauki gyada zai kai wani wuri, sai ya zo shingen sojoji, suka tsaida shi ya yi masa Ingilish ‘weting  for  inside’ wato mene ne a ciki?  Babarbare bai jin Ingilish, amma wai dole ya yi, sai ya ce  Oga  gurnet  ne (yana nufin groundnot wato gyada). Aka ce da shi “Come down!” ya sako aka fara dukansa, sai ya ce a bari zan fada da Hausa. Gyada na dauko sai suka ce masa  groundnut  za ka ce ba gurnet ba. Da aka sake shi ya ja mota, daga nan idan ya zo shingen soji kafin  a tambaye shi me ya dauko, sai ya ce gyada ne oga.
Daga Garba Sabiyola, Gashuwa, Jihar Yobe  07066581437