Zan fi mayar da hankali wajen kara wa APC yawan mambobi – Ganduje
Tsohon gwamnan na Kano ya ce zai inganta shugabancin jam’iyyar.
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce zai fi mayar da hankali wajen ganin karin mutane sun shiga jam’iyyar APC idan ya zama shugabanta na kasa.
Ganduje, ya bayyana haka ne a lokacin da shugabannin matasan jihohi 36 na jam’iyyar suka ziyarce shi a Abuja.
- Waiwaye: Sau nawa aka taba yin juyin mulki a Nijar?
- Alhassan Doguwa ya zama shugaban kwamitin man fetur na Majalisa
Ganduje ya kuma ce zai kawo gyare-gyare a jam’iyyar.
Ya ce, “Yayin da muke aiki don inganta Dimokuradiyya, a lokaci guda kuma za mu kawo sauye-sauye masu kyau ga jam’iyyar domin dorewar Dimokuradiyya da ci gaba.
“Za mu bai wa samar wa jam’iyya sabbin mambobi fifiko. Zan gabatar da dabarun magance rikice-rikice don inganta jam’iyyarmu. Jihohin da ba su da gwamnatocin APC za a ba su kulawa ta musamman.”
Da yake magana a madadin shugabannin matasan, shugabansu na kasa a jam’iyyar, Adebayo Israel ya ce, “Yallabai muna goyon bayan ka zama shugaban jam’iyyarmu na kasa. Wannan ya dace kuma yana kara tabbatar mana da jam’iyyar na tafiya kan tafarki”.
“Mai girma Gwamna, wannan ci gaban tunani ne mai kyau. Muna ba ku tabbacin cewa, za mu yi aiki ba dare ba rana don tallafa wa shugabancinka a kowane mataki.”