Zan gina alkaryar nishadi a Osun – Zababben Gwamna Adeleke
Ya ce harkar za ta kawo wa jihar kudin shiga
Zababben Gwamnan Jihar Osun Ademola Adeleke ya ce, bangaren nishadi na cikin abubuwan da gwamnatinsa za ta ba wa fiffiko.
Ademola Adeleke ya bayyana haka ne a zantawarsa da tashar talabijin ta Channels, inda ya ce Jihar Osun na da dimbin al’adu da ya kamata a bunkasa su.
- Yajin aikin ASUU: Yadda muke rayuwa ba tare da albashi ba — Malaman jami’a
- Ana zanga-zanga kan sauya kundin tsarin mulki a Tunisiya
Don haka akwai yiwuwar gwamnatinsa za ta gina alkaryar nishadi ta yadda dan yayansa, Davido da kuma dansa B-Red za su samu damar gabatar da shirye-shiryen wakoki da raye-rayen da za su samar wa jihar kudin shiga.
“Najeriya na sahun gaba wajen al’adu a Afirka don haka Jihar Osun za ta yi amfani da wannan dama don bunqasa bangaren nishadi.
“Yanzu a ce Davido da B-Red da sauran mawaka za su zo su yi wasa a wannan alqaryar, ai ba qaramin kudin shiga hakan zai samar wa jihar Osun ba, don haka wannan na cikin ayyukan da za mu gabatar nan ba da jimawa ba,” inji shi.
A ranar Asabar da ta gabata ce aka yi zaben Gwamnan Jihar Osun, inda Adeleke ya doke Gwamnan Jihar Gboyega Oyetola na Jam’iyyar APC