Zan iya auren dan fim – Belinda Effah

daya daga cikin mata ’yan fim na Kudancin Najeriya da ke tashe a zamanin nan, Belinda Effah ta bayyana cewa idan wani abokin sana’arta dan fim ya nuna tabbacin kyakkyawar kauna a gare ta, babu abin da zai hana ta amince da aurensa.’Yar fim din wacce tun daga farkon shigar ta harkar ta fara da […]

Zan iya auren dan fim – Belinda Effah

daya daga cikin mata ’yan fim na Kudancin Najeriya da ke tashe a zamanin nan, Belinda Effah ta bayyana cewa idan wani abokin sana’arta dan fim ya nuna tabbacin kyakkyawar kauna a gare ta, babu abin da zai hana ta amince da aurensa.
’Yar fim din wacce tun daga farkon shigar ta harkar ta fara da fim din ‘Udeme mmi’ ta ce wani lokaci idan aka hada ta da namiji a wani fim din soyayya takan tsaya ne kawai a matsayin ’yar wasa, wato ba ta jin cewa da gaske ne a zahiri. “Idan ana batun soyayya ta zahiri kuwa, ba ni da zabi ga duk wanda ya nuna mini kauna ta zahiri. Idan har na samu wani namiji dan fim ya nuna mini kauna sosai kuma na tabbata da gaske yake, zan iya amincewa da shi mu yi aure.” Inji Belinda.
Da aka tambaye ta ko an taba yaudarar ta a soyayya, sai ta amsa da cewa: “kwarai kuwa, an taba yaudara ta, an taba karya mini zuciya a soyayya. Ni ma ba zan ce ban taba karya zukatan wasu ba. Don haka babu damuwa, domin irin haka na yawan faruwa a yawan lokuta da dama. Wani lokaci za ka gamu da mai son ka, wani lokaci kuwa akasin haka. Hakan ba yana nufin babu soyayya ta kwarai ba.”
Belinda dai ta samu daukaka a fannin fim, musamman a bara ne ta ci kambin AMAA, inda aka zabe ta a matsayin ’yar fim din da ta zarce kowa cikin taurari mata masu tasowa a 2013.