Zan iya kwada wa saurayina mari a kan ‘bestie’ — Budurwa
“Shi saurayi za ta iya rabuwa da shi idan ta auri wani, amma ni ko tayi aure muna fatan zumuncinmu ya ci gaba.”
Wata budurwa ta bayyana cewa za ta iya sa hannu ta zabga wa saurayinta mari matukar ya yi yunkurin taba martabar alakar da ke tsakaninta da ‘bestienta’.
Galibi dai ana amfani da kalmar bestie ne ga wani wanda yake zama matsayin babban aboki ga budurwa, amma ba saurayinta ba ne, kai hasali ma kusancinsu ya kan fi na saurayinta.
Budurwar ta bayyana haka ne lokacin da ake ta cece-kuce a kan irin matsayin besty a wurin ’yan matan zamani, inda ake ganin bestie na zama tamkar wani sashe na rayuwar wadda ya ke alaka da ita.
Ta bayyana haka ne a dandalin sada zumunta na Facebook, lokacin da take tsokaci a kan maudu’in na bestie, inda ta ce babu wani tunani da za ta yi don ta mari saurayi a kan bestie, saboda ta ce, “Bestie shi ne rabin rayuwar mace, don haka ba zai yiwu a yi wasa da rabin rayuwa ba.”
Har ila yau ta ce, “Za ka iya zagin saurayina na kyale ka, amma ka ga bestie, kar ka sake ka zage shi a gaba na.
“Ni fa wallahi tsakani da Allah ko fada muka yi da baby [saurayina] ya bata min rai, bestie nake kira yake rarrashi na,” inji budurwar.
Alakar da ke tsakanin bestie da budurwa a wannan lokacin ne ya sa ’yan mata suka ba shi wani muhimmin matsayi da ko saurayi ko miji ba shi da shi a rayuwarsu.
Duk da cewa ba soyayya ake da shi ba, amma shi ke zama babban mai zartarwa a rayuwar wadda suke da alaka da ita; shi ke da ikon ya ce a yi ko ya hana.
Da yake tsokaci a kan yadda alakar bestie take kasancewa, wani matashi, Aliyu Jalal, ya ce shi ma bestie ne na mata har guda biyu.
“Daya daga ciki ma budurwar babban abokina ce, kuma ni na hada alakar. To idan daya daga cikinsu na da matsala da dayan, su kan tuntube ni domin na yi masu sulhu,” inji shi.
Ya kara da cewa ita kuma dayar kawarsa ce tun suna makarantar sakandire har su ka je jami’.
“Idan har ta na neman shawara a kan komi, ni take tuntuba. Tana fada min abubuwan da ba za ta iya fada wa saurayinta ba, saboda shi saurayi za ta iya rabuwa da shi idan ta auri wani, amma ni ko tayi aure muna fatan zumuncinmu ya ci gaba saboda da kyakkyawar niyya muka kulla.”
Da muka tuntunbi Fatima Fouad Hashim, mai shafukan Open Diaries a dandalin sada zumunta kuma mai sharhi kan al’amuran zamantakewar masoya, ta ce ta wallafa wani korafin da wata budurwa ta tura mata game da saurayinta na rashin saya mata kayan kwalliya wanda sai dai bestienta ne yake sayamata.
A cikin korafin, budurwar ta bayyana cewa a dokar gidansu, ba a bari budurwa ta karbi kudin saurayi kai tsaye har sai an yi baikonta.
Wannan ya sa saurayin ba ya bata kudi kuma ya bata ma ba za ta karba ba, amma kuma sai ta ce: “Ai shi ya san abin da ya dace, dan kayan kwalliyar nan da zobe haka, cakuleti da ‘ice cream’ ko turare haka ba sai kaba wa mutum kudi ba, ihsani ne tsakanin masoya kusan duk wadannan abubuwan yanzu bestiena ne yake kawominsu a matsayin kyauta”
Abdullahi Ogabo Atazo shi ma ya bayyana yadda ya fada tarkon wata budurwa inda sai da ya yi da gaske kafin ya samu kufcewa daga wannan matsayi da ta ba shi, duk da shi daga karshe ta bayyana cewa tana son sa da aure wanda hakan ya sa suka rabu gaba daya.
Sai dai wasu na ganin wannan sabuwar alaka a matsayin mara kyau, kuma za ta iya kai masu yinta ga halaka
Wasu ma kai tsaye suka alakanta abin da Yahudanci wanda ya fara samo asali daga jami’o’i kamar yadda Habib Ahmad ya bayyana.