Zan kada danjuma Goje a zaben Sanata –Usman Bello Kumo

dan Majalisar Tarayya daga mazabar Akko a Jihar Gombe da ke son tsayawa takarar Sanata a zaben 2015, Alhaji Usman Bello Kumo (World ) ya ce zai kayar da Sanata Muhammad danjuma Goje na Jam’iyyar APC a zabe. dan Majalisa Usman Bello Kumo ya bayyana haka ne a Gombe a lokacin da yake ganawa da […]

Zan kada danjuma Goje a zaben Sanata –Usman Bello Kumo
Zan kada danjuma Goje a zaben Sanata –Usman Bello Kumo

dan Majalisar Tarayya daga mazabar Akko a Jihar Gombe da ke son tsayawa takarar Sanata a zaben 2015, Alhaji Usman Bello Kumo (World ) ya ce zai kayar da Sanata Muhammad danjuma Goje na Jam’iyyar APC a zabe.

dan Majalisa Usman Bello Kumo ya bayyana haka ne a Gombe a lokacin da yake ganawa da manema labarai bayan ganawarsa da shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Alhaji Ahmad Yayari, lokacin da ya kai masa ziyarar godiya kan damar da jam’iyyarsu ta PDP ta ba shi na
ya tsaya takarar Sanata daga mazabar Gombe ta Tsakiya.
Usman Kumo ya ce abin da ya sa ya ce zai kada Sanata Goje a zabe shi ne saboda shirin da yake da shi da kuma irin ayyukan raya kasa da taimakon jama’a da ya yi a yankin karamar Hukumar Akko a zamansa a Majalisar Tarayya na shekara hudu.
Game da rade-radin cewa Jam’iyyar PDP ba ta tsayar da shi takarar Sanata ba, kuma akwai yiwuwar zai canja sheka zuwa Jam’iyyar APC, ya ce shi cikakken dan PDP ne kuma PDP ta yi masa riga da wando, saboda ya kasance shugaban karamar hukuma sau biyu a PDP ya zama sakataren hukumar zabe kuma yanzu yana dan Majalisar Tarayya, don haka wannan batu labarin kanzon kurege ne.
Alhaji Usman Kumo, ya ce daga lokacin da ya zama dan Majalisar Tarayya ya kawo abubuwan ci gaba a yankinsa kamar gina ofishin ’yan sanda na Naira miliyan 30 a hedkwatar karamar hukumar wato Kumo da gina cibiyar lafiya ta Naira miliyan a garin bula da wata cibiyar lafiya ta Naira miliyan 21 a garuruwan Taliyawa da Gujuba da Kembu.
Ya ce ya samar da rijiyoyin burtsatse da sama wa matasa kimanin 170 aikin dan sanda da masu mukamin ASP 17.