Zan kada Gwamnan Jihar Kebbi a zaben Sanata – Dokta Abdullahi

dan takarar Sanatan mazabar Kebbi ta Arewa a karkashin Jam’iyyar APC Dokta Yahaya Abdullahi ya ce zai kayar da Gwamnan Jihar Alhaji Sa’idu Usman Nasamu dakingari na Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa. dan takarar wanda tsohon Babban Sakatare ne a Ma’aikatar Raya Yankin Neja-Delta ya bayyana haka ne a garin Argungu lokacin da yake […]

Zan kada Gwamnan Jihar Kebbi a zaben Sanata – Dokta Abdullahi
Zan kada Gwamnan Jihar Kebbi a zaben Sanata – Dokta Abdullahi

dan takarar Sanatan mazabar Kebbi ta Arewa a karkashin Jam’iyyar APC Dokta Yahaya Abdullahi ya ce zai kayar da Gwamnan Jihar Alhaji Sa’idu Usman Nasamu dakingari na Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa.

dan takarar wanda tsohon Babban Sakatare ne a Ma’aikatar Raya Yankin Neja-Delta ya bayyana haka ne a garin Argungu lokacin da yake ganawa da manema labarai, inda ya ce Jam’iyyar PDP a jihar yanzu ta zama gidan gara kana zuba mata ruwa kasa za ta yi, domin kuwa rikicin da PDP ta shiga a jihar nan da shekara goma a gaba ba za ta iya warware shi ba.
Dokta Abdullahi ya kuma ce duk wanda ke cikin Jam’iyyar PDP ba wanda Gwamna dakingari bai bata masa rai ba, saboda ko zabubbukan fidda gwani da PDP ta yi kujerun majalisar jiha ba wanda ba a canza ba bayan zaben fidda gwani, shi ko zaben fidda gwani na Gwamna ba a taba tafka rashin adalci irinsa ba saboda ko zaben ba a yi ba.
Ya ce wannan rashin adalci da aka yi wa ’yan takarar PDP a Jihar Kebbi zai kara ba shi damar dankara Gwamnan da kasa a zaben Sanata da za su gwabza.