Zan kafa masana’antar yin batir a Najeriya – Namakaram

Wani  fitattacen mai sana’ar gyaran baturan mota da ke zaune a garin Jos, fadar Jihar Filato, Alhaji Ibrahim Namakaram ya bayyana cewa yana nan yana shirin bude masana’antar yin batir tasa ta kansa a Najeriya.  Alhaji Ibrahim Namakaram ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a garin Jos. Alhaji Ibrahim Namakaram […]

Zan kafa masana’antar yin batir a Najeriya – Namakaram

Wani  fitattacen mai sana’ar gyaran baturan mota da ke zaune a garin Jos, fadar Jihar Filato, Alhaji Ibrahim Namakaram ya bayyana cewa yana nan yana shirin bude masana’antar yin batir tasa ta kansa a Najeriya. 

Alhaji Ibrahim Namakaram ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a garin Jos.

Alhaji Ibrahim Namakaram ya ce wannan sana’a ta gyaran baturan mota da ya fara sama da shekara 33 da suka gabata, ana kawo musu gyaran baturan mota da baturan sola daga wurare daban daban. Kuma ana  kawo musu baturan da aka yi amfani da su daga Turai, su saya su tayar da su  sannan su sayar. 

“Babu shakka mun  samu nasarori da dama a cikin wannan sana’a ta gyaran batur. Domin a halin yanzu akwai sama da mutum 70, da suke cin abinci a karkashina. Sannan na samu nasarar  bude wuraren  yin wannan sana’a har guda biyar  a cikin  garin  Jos. Haka  na bude harkar sufurin manyan motoci duk ta dalilin wannan sana’a,’’ inji shi

Ya yi  kira ga gwamnati ta tallafa wa masu sana’ar gyaran batur, domin wannan sana’a tana da matukar muhimmanci.