Zan kammala aikin tashar jiragen ruwa ta Baro idan kuka zabe ni – Atiku
Ya kuma yi ak]lkawarin magance matsalar tsaro a Neja
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi alkawarin kammala aikin tashar jiragen ruwa ta Baro da ke Jihar Neja, muddin aka zabe shi a zabe mai zuwa.
Atiku ya kuma ce jam’iyyarsa ce kawai take da siddabarun da za ta magance kalubalen tsaro da ya addabi kasar, musamman ma Jihar Neja.
- Mutum 8 cikin kowanne 10 a China na dauke da COVID-19 – Rahoto
- Burkina Faso ta ba sojojin Faransa wata daya su fice daga kasarta
Ya yi wadannan alkawuran ne lokacin da yake jawabi ga wasu kusoshi da magoya bayan jam’iyyar a Minna, babban birnin Jihar Neja ranar Asabar.
Atiku ya ce PDP ce ta faro aikin na Baro rimi-rimi lokacin da take mulki, amma APC na zuwa ta yi watsi da shi.
A cewar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, “Muna addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya a Jihar nan. Kun san PDP ce kawai za ta iya dawo da zaman lafiya a Neja. Lokacin da take mulki daga 1999 zuwa 2015, akwai matsalar tsaro a Neja? Muna so mu tabbatar muku cewa muddin PDP ta dawo, matsalar za ta zama tarihi.
“Muna kuma so mu tabbatar muku cewa aikin tashar Baro da PDP ta fara, amma aka yi wasti da shi lokacin da kuka bukaci canji, yanzu kun ga canjin ko? Me suka canza? Matsalar tsaro, tsadar rayuwa ko matsin tattalin arziki?
“Muna rokonku ku dawo PDP saboda ingantuwar al’amuran tsaro da ci gana Jihar Neja da ma na Najeriya baki daya,” in ji Atiku.
Shi ma a nasa jawabin, Shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, wanda ya karbi tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar, Ahmad Musa Ibeto da dubban magoya bayansa, ya ce Allah Ya albarkaci Jihar da dimbin ma’adinai.
“Amma abin takaici, duk da wadanna tarin ni’imomin, APC ta mayar da ita hedkwatar talauci da rashin zaman lafiya. Akwai lokuta da ma wasu sassan wannan Jihar suka koma karkashin ’yan bindiga. Idan kuka zabe mu, za mu kawo ci gaba mai amfani,” in ji Ayu.