Zan kammala ayyukana kafin 2015 – Kwankwaso

Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ba da tabbacin zai kammala dukkan ayyukan da ya faro kafin karewar wa’adin mulkinsa a shekarar 2015. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da ’yan kwangilan da ke gudanar da manyan ayyuka a jihar dab da zai tashi zuwa aikin Hajjin bana.Gwamna Kwankwaso […]

Zan kammala ayyukana kafin 2015 – Kwankwaso

 Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, Gwamnan Jihar KanoGwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ba da tabbacin zai kammala dukkan ayyukan da ya faro kafin karewar wa’adin mulkinsa a shekarar 2015. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da ’yan kwangilan da ke gudanar da manyan ayyuka a jihar dab da zai tashi zuwa aikin Hajjin bana.
Gwamna Kwankwaso ya ce gwamnatinsa na da isassun kudi da kuma karfin da za ta iya tabbatar da kammala ayyukan da ta faro, don haka ya nanata cewa gwamnatinsa ba za ta bar wani kwantai na aiki ga gwamnatin da za ta gaje ta ba. “Burinmu shi ne mu kammala wadannan ayyuka a kan lokaci, kuma da gaske muke a kan wannan magana. Saboda haka duk wanda muka kama da laifi game da kin gudanar da ayyyukan za mu ladabtar da shi,” inji shi.
Gwamnan ya kara da cewa”Duk da cewa muna son ganin mun kammala ayyukanmu a kan lokaci, wannan ba ya nufin za mu yarda da ayyuka marasa inganci. Tsarin wannan gwamnat shi ne dole a kammala kwangilolin da muka bayar a kan lokacin da aka yi alkawari.”
Gwamnan ya ba ’yan kwangilar tabbacin biyan su kudinsu a duk lokacin da suka nemadon ganin an kammala ayyukan a kan lokaci.