Zan kara Ministoci-Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai kara yawan Ministoci domin su kara yawa a Majalisar Zantarwa. Shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata, a lokacin da yake zantawa da Kwamitin Zantarwar Jam’iyyar APC a Abuja. Ya ce zai kara yawan ‘yan Majalisar Zatarwar ne domin a samu sabbin mutane, kuma su […]

Zan kara Ministoci-Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai kara yawan Ministoci domin su kara yawa a Majalisar Zantarwa.

Shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata, a lokacin da yake zantawa da Kwamitin Zantarwar Jam’iyyar APC a Abuja.

Ya ce zai kara yawan ‘yan Majalisar Zatarwar ne domin a samu sabbin mutane, kuma su shigo da sabbin tsare-tsare.

A yanzu dai Buhari na da ministoci 36, daya daga kowace jiha.

Hakanan kuma, shugaba Buhari ya nuna rashin dadinsa bisa yadda har yanzu bai sanya sabbin shugaban wasu bangarorin gwamnatin tarayya ba, inda ya ce hakan ya faru ne saboda wasu dalilai.

Sannan ya ce da yardar Allah kwanan nan za a sanar da sabbin mukaman, musamman ganin yadda tattalin arziki ke farfadowa a yanzu.