Zan karbo duk kadarorin gwamnati da Ganduje ya sayar ba bisa ka’ida ba – Abba

Ya bayyana hakan ne bayan an rantsar da shi a Kano

Zan karbo duk kadarorin gwamnati da Ganduje ya sayar ba bisa ka’ida ba – Abba

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin karbo duk wasu filaye da gidaje mallakin gwamnatin Jihar da aka mallaka wa wasu tsirarun mutane ba bisa kaida ba.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi jim kadan bayan an rantsar da shi a matsayin sabon Gwamnan Jihar.

A ranar Litinin ce da Alkalin-Alkalan Jihar, Mai Shari’a Dije Audu Aboki ta rantsar da Gwamnan tare da Mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam, a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Kano.

Abba ya kuma ce gwamnatinsa za ta dawo da auren zawarawa a jihar.

Har ila yau, Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta daina karbar haraji daga masu kananan sana’o’i, musamman wadanda suke sayar da kayayyakin kasa da Naira 50.

Dubban magoya bayan Jamiyyar NNPP ne suka halarci bikin rantsuwar da aka a yi a Kano.