Zan karya kwarin rashin tazarce a Jihar Oyo – Gwamna Ajimobi

A karshen makon da ya wuce ne, Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo, ya bayyana aniyarsa ta sake tsaya takarar gwamnan jihar a karo na biyu, inda ya bayyana cewa takararsa amsa gayyatar matasan jihar ne da suka fito daga knaanan hukumomi 33.Matasa maza da mata da suka fito daga kananan hukumomi 33 suka yi […]

Zan karya kwarin rashin tazarce a Jihar Oyo – Gwamna Ajimobi
Zan karya kwarin rashin tazarce a Jihar Oyo – Gwamna Ajimobi

A karshen makon da ya wuce ne, Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo, ya bayyana aniyarsa ta sake tsaya takarar gwamnan jihar a karo na biyu, inda ya bayyana cewa takararsa amsa gayyatar matasan jihar ne da suka fito daga knaanan hukumomi 33.
Matasa maza da mata da suka fito daga kananan hukumomi 33 suka yi jerin gwano daga babban  zauren taro na Mapo da ke tsakiyar birnin Ibadan zuwa gidan gwamnati a Agodi, domin mika bukatar tasu hannu da hannu ga Gwamnan.
Da gwamnan yake mayar da jawabi kan bukatar da matasan suka gabatar masa, ya yi nuni da irin ayyukan raya kasa da ya gudanar, wadanda ya ce Gwamnatin PDP a jihar ta kasa yi.
“Daga ranar 29 ga wannan wata, za mu fito domin bude dukkan ayyukan ci gaban jama’a da muka gudanar cikin kankanen lokaci. Za mu yi amfani da wannan dama wajen shaida wa al’ummar Jihar  Oyo irin rawar da muka taka, domin amfaninsu tare da tabbatar musu cewa, zan sake fitowa takara domin rike wannan kujera wacce za mu yi nasara idan Allah ya yarda.” Inji Gwamna Ajimobi.
Mutane biyu Mista Balogun Abiodun da Mista Ambali Abiodun, su ne suka yi bayanai a madadin matasan. Sun ce, kafin Gwamna Ajimobi ya haye bisa karaga a shekara ta 2011, Jihar Oyo, ta samu kanta cikin wani irin halin damuwa da jama’a suka samu kansu a ciki a dalilin rashin iya tafiyar da mulki da tashe tashen hankula a sassa daban-daban na Jihar.
“Amma daga lokacin da Gwamna Ajimobi, ya kama ragamar mulki, sai ya fito da salon mulki mai alkibla wanda ya dace da rayuwar miliyoyin mutane kuma yayi maganin miyagun ayyukan ‘yan banga da suka mamaye birnin Ibadan suna cin karensu babu babbaka a wancan lokaci. Saboda haka muka fito domin nuna goyon baya ga wannan salon muki da muke fatan za ka ci gaba da yin irinsa domin amfanin Jihar Oyo da kasa baki daya,” a cewarsu.

…Za mu kada kai a zabe mai zuwa- Jigon PDP

Labarai daga Kabir Yayo Ali, a Ibadan,

Wani jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Oyo, Alhaji danjuma Yakubu ya kalubalanci tazarcen Gwamna Abiola Ajimobi a tutar jam’iyyar APC, inda ya bayyana cewa tuni ya bata rawarsa da tsalle, saboda rusa gidajen al’umma ba tare da biyansu diyya ba; ga kama ’yan talla a tituna, ana tsula musu bulala, sannan a kwace kayansu.
“Wanda ya aikata ayyukan takura wa jama’a da sunan gyaran gari, shi ne zai yi tazarce?” inji shi.
A hirarsa da Aminiya a Ibadan, Alhaji danjuma Yakubu, ya ce, yanzu haka mutanen da aka rusa musu gidaje da shaguna da wadanda aka kore su daga wuraren da suke cin abinci ba tare da sama musu wani wuri daban ba, suna nan suna cikin halin ni ‘yasu. “abin da muke so ayi shi ne, a biya diyya ga mutanen da aka rusa gidajensu, kuma a samar da sababbin wurare ko kasuwanni da kananan ‘yan kasuwa za su baje kolinsu, domin samun walwalar rayuwa a cikin irin wannan hali da Najeriya take ciki.”
Ya kuma bayyana aniyarsu ta dawo da tsohon Gwamna Adebayo Alao Akala, wanda ya sha kaye a zaben shekara ta 2011. “Yanzu ne al’ummar Jihar Oyo, suka gano cewa, babu Gwamnan da ya taba yi musu aiki tsakani da Allah kamar Adebayo Alao Akala, shi ne dalilin da yasa muka fara shirin dawowar shi bisa karaga a zabe mai gabatowa da PDP za ta fatattaki APC a jihar.”
Da aka tuntube game da masu suayin sheka daga PDP zuwa APC, sai ya ce, “magoya bayan PDP a sassa daban-daban na Jihar Oyo, suna nan ba su je ko ina ba. Sun yi amfani da sunayen wasu baragurbin mutane daga cikinmu ne suke yi wa mutane karya. Wannan ba zai taba ba mu tsoro ba. Idan ka lura za ka iya fahimtar cewa, rikicin da ya dabaibaye APC shi ne ya koro dimbin magoya bayanta da suke ficewa suna shigowa cikin PDP, wanda alama ce ta kasawarsu. Idan kaga jam’iyarmu PDP har ta kasa cin zabe a shekara ta 2015 to, ba a tsayar da dan takara kamar Adebayo Alao Akala ba ne.”