Zan kawo gyara idan na zama Shugaban PDP-Farfesa Tunde Adenira
Tsohon Minista a Najeriya Farfesa Tunde Adeniran ya tabbatarwa ‘ya’yan jamiyyarsu ta PDP cewa zai kawo gyaran kura-kuran da suka yi a baya. Farfesa Adeniran ya bayyana hakan a yau Alhamis lokacin da take ganawa da wakilan jamiyyarsu (Delegate) daga shiyar Arewa maso Gabas da suka tare shi a Gombe. Ya ce kura-kuran da suka […]

Tsohon Minista a Najeriya Farfesa Tunde Adeniran ya tabbatarwa ‘ya’yan jamiyyarsu ta PDP cewa zai kawo gyaran kura-kuran da suka yi a baya.
Farfesa Adeniran ya bayyana hakan a yau Alhamis lokacin da take ganawa da wakilan jamiyyarsu (Delegate) daga shiyar Arewa maso Gabas da suka tare shi a Gombe.
Ya ce kura-kuran da suka yi a baya shi ya kawo faduwar su a zabe amma yanzu za a gyara don su sake karbar mulkin kasar daga hannun APC.
Shi ma wani jigo a tafiyar Sanata Nasiru Ibrahim Mantu, cewa ya yi zaluncin da suka yi lokacin suna mulki shi ya kawo faduwar su a zabe ba APC ce ta kadasu ba.
Mantu ya kuma ce yanzu sun kawo sabon fuska be Wanda ganinsa zai jama’a su gane cewa sunyi kuskure shi yasa suka dauko Tunde Adeniran.
Ita Hajiya Zainab Maina, cewa ta yi PDP ta yi aiki na shekara goma sha shida a Najeriya amma daga baya sai tayi kuskure Allah ya samu suka fadi Wanda yanzu suke shirin gyarawa.
Zainab Maina wacce tsohuwar Minista ce daga jihar Yobe, tace da sun dauki Kansu wasu kananan Alloli wadanda ake yiwa bauta shi kuwa Allah ya nuna musu kuskurensu.
Sanata Sa’idu Umar Kumo, karfafa cewa yayi yanzu PDP za ta dawo cikin hayyacin ta saboda ta sake salon gyara.
Sanata Kumo, ya kara da cewa duk da jamiyyarsu ta fadi a zabe amma duk Najeriya babu mazabar da basu da zababbe Wanda yaci zabe a PDP.
Kamfen din na Farfesa Adeniran kamfen ne da ya samo shi daga jihar Gombe bayan da ya mika fom dinsa na takara jiya a sakatariyar jamiyyar dake Abuja.