Zan kayar da Gwamna Jang a zaben Sanata – Unice Sambo

’Yar takarar kujerar Sanata ta mazabar Filato ta Arewa a karkashin Jam’iyyar APC, Misis Unice Ayisa Sambo ta ce da yardar Allah za ta kayar da Gwamnan Jihar Filato Mista Jonah Jang da ke takarar wannan kujera a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben da za a gudanar a ranar 28 ga Maris mai zuwa.  Misis […]

Zan kayar da Gwamna Jang a zaben Sanata – Unice Sambo
Zan kayar da Gwamna Jang a zaben Sanata – Unice Sambo

’Yar takarar kujerar Sanata ta mazabar Filato ta Arewa a karkashin Jam’iyyar APC, Misis Unice Ayisa Sambo ta ce da yardar Allah za ta kayar da Gwamnan Jihar Filato Mista Jonah Jang da ke takarar wannan kujera a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben da za a gudanar a ranar 28 ga Maris mai zuwa. 

Misis Unice Ayisa Sambo ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da manema labarai a cibiyar ’yan jarida da ke Jos, inda ta ce duk da PDP na amfani da kudin gwamnati da ma’aikatanta wajen yakin neman zabe, babu shakka za ta samu nasara a takarar domin al’ummar mazabar sun gaji da rikice-rikice, kuma sun ga rashin adalci da yaudarar da aka yi musu.
Ta ce “Rikice-rikicen da muka yi fama da su a wannan mazaba, sun lalata mana komai musamman harkokin kasuwanci, kowa ya gaji da irin wannan zama saboda haka kowa yana bukatar canji. Duk wuraren da na shiga yakin neman zabe, mutane sun fito sun karbe ni hannu bibbiyu tare da nuna goyan baya gare ni saboda suna bukatar canji. Mun shiga cikin Hausawa a Unguwar Rikkos da Unguwar Rogo da Bauchi Road da ke cikin garin Jos, kuma an karbe mu.”
Kuma ta ce sun je sauran sassan mazabar ko’ina mutane sun karbe su. “Wannan jiha tamu ce baki daya, kuma kowanne dan jihar nan yana da damar ya fito ya tsaya kowace irin takara, don haka babu wanda ya isa ya hana ni ko ya tsorani kan wannan takara da nake yi,” inji ta.
Misis Sambo ta ce da yardar Allah idan suka samu nasara za su tabbatar cewa sun hada kan al’ummar mazabar, domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kuma za su samar wa matasa aikin yi da ruwa da bunkasa ilimi da harkokin kiwon lafiya da aikin noma.