Zan koma Borno don agaza wa jama’a – Jami’ar Agaji da Boko Haram suka sako
A ranar 22 ga Disamban bara ne wadansu da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne suka sace wadansu ma’aikatan agaji ciki har da wata jami’ar kiwon lafiya ’yar asalin Jihar Filato, mai suna Jenepher Samuel Ukambong da take aikin tallafa wa jama’a kan kiwon lafiya a Manguno da ke Jihar Barno karkashin wata kungiyar […]
A ranar 22 ga Disamban bara ne wadansu da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne suka sace wadansu ma’aikatan agaji ciki har da wata jami’ar kiwon lafiya ’yar asalin Jihar Filato, mai suna Jenepher Samuel Ukambong da take aikin tallafa wa jama’a kan kiwon lafiya a Manguno da ke Jihar Barno karkashin wata kungiyar Allance for International Medical Action (AIMA). A wannan mako ne aka sako jami’ar. Wakilinmu ya je kauyen Gura Topp da ke kusa da garin Bukur a Karamar Hukumar Jos ta Kudu gidan iyalan jami’ar, inda suka tattauna kan abubuwan da suka faru, har zuwa lokacin da aka sako ta:

Ma ye karfafa miki gwiwa kika tafi Jihar Borno don aikin agaji, duk da halin da yankin ke ciki na yake-yaken Boko Haram?
Babban abin da ya ba ni karfin gwiwar tafiya wannan yanki, shi ne domin in je in taimaka wa mata masu ciki, domin su haihu lafiya kuma in taimaka wa kananan yaran da aka haifa. Kuma kamar yadda bayanai suka gabata, ni mai aikin ungozoma ce tare da kula da kiwon lafiyar kananan yara. Domin ni tunda na taso, mai son kananan yara ce da aikin ungozoma, wato taimaka wa mata masu ciki a wajen haihuwa.
Kafin in tafi wannan yanki, akwai abokan aikinmu da suke aiki a can, wadanda suka san ni kuma suka san halayena, don haka suka nema mini aiki a can, na samu kuma na tafi.
Yaya kuke gudanar da aikin a can, ganin halin da ake ciki na yake-yaken Boko Haram?
A wajen da muke gudanar da aikinmu, an samar da tsaro sosai. Don haka mutane suke samun zuwa wurin, domin ba don an samar da tsaro sosai ba, mutane ba za su iya zuwa wajen ba saboda halin da ake ciki a yankin. Da taimakon wannan tsaro da aka ba mu muke samu muke gudanar da ayyukanmu a yankin.
Me ya faru ko ya gudana a yayin da aka dauke ku, aka yi garkuwa da ku?
Mun taso daga garin Munguno, a hanya za mu tafi Maiduguri ne suka tare motarmu, suka fitar da mu suka tafi da mu, mu takwas. Kuma sai da suka harbe wadansu a wajen, kafin su dauke mu.
Yaya rayuwarku ta kasance lokacin da kuke hanun ’yan Boko Haram?
A lokacin da suka tafi da mu daji, sun je sun ajiye mu a wani daki suna ba mu abinci danye da ita ce, muna dafawa da kanmu muna ci. Kuma suka ce mana duk abin da muke so, mu tambaya za su ba mu. Babu wani mummunan abu da suka yi mana. Haka muka ci gaba da rayuwa, har lokacin da suka sake mu.
Akwai Leah Sharibu da wadansu mata da maza da suke hannun ’yan Boko Haram, ko kin gan su a wajen da aka tsare ku?
Ni mace daya ce kawai na gani a wajen da ake kira Alice Loksha Ngadda. Ita ma jami’ar kiwon lafiya ce da take aikin agaji a wannan yanki a karkashin Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF). Kuma ’yan Boko Haram din sun tafi da ita ce a lokacin da suka kai hari kauyen Raan da ke Jihar Barno, tun a ranar 1 ga Afrilun 2018. Ita ce kawai na gani a wajen.
Yaya aka yi suka sako ku, ko gudowa kuka yi?
Yadda aka yi wadannan mutane suka sako mu shi ne, muna zaune bayan mun yi kwana 24 a wajensu, sai kawai muka ji sun ce mu fito za a sake mu. Da muka fito muka yi tafiya a kafa, ba mu fi minti biyar ba, sai muka ga mota, suka zuba mu a ciki. Wani ya tuka motar ya fito da mu, ba mu san ko wane ne ba, ya kai mu ofishin DSS a Maiduguri.
Da ma jami’an na DSS sun kira jami’an kungiyar da nake yi wa aiki, kan su zo su karbe ni. A nan jami’an na DSS suka mika ni ga jami’an kungiyar. Su kuma suka dauke ni zuwa Abuja, inda iyalina suka zauna suna jira, suka mika ni ga iyalina daga nan muka taso muka iso Jos.
Kamar ku nawa ne suka sako a wannan lokaci?
Mu biyar ne suka sako, mata biyu maza uku.
Ko sun tilasta ki don ki amshi Musulunci, kamar yadda suka yi wa Leah Sharibu?
Mu dai sun ce mana za su yi mana nasiha ce kuma kafin su yi mana wannan nasiha, sun yi mana bayani kan addinin Musulunci amma ba su ce mana dole mu musulunta ba.
Wadannan mutane kina ganin suna yin wannan abin ne da son su ko ana sanya su ne?
To, ni dai sun ce mana Alkur’ani ne ya ce su yi haka. Ni dai maganganun nasu sun yi yawa, don haka ban iya rikewa ba.
Yaya kika ji lokacin da mutanen suka tafi da ku?
Gaskiya na ji tsoro sosai amma daga baya na mayar da komai ga Allah, tunda Shi ne Mai kowa Mai komai. Don haka na mika komai a gare shi, kan wannan al’amari.
Ganin yadda wannan abu ya faru, kina tunanin za ki sake komawa yankin, domin ci gaba da wannan aiki?
Wannan abu da ya faru bai karya mini gwiwa ba, don haka a shirye nake in sake komawa wannan wuri, domin in ci gaba da taimaka wa mutanen wannan wuri. Ganin irin bukatar da suke da ita, na a taimaka musu, musamman kan harkokin kiwon lafiya. Don haka bai kamata kowa ya gudu ya bar su ba saboda halin da wannan yanki yake ciki. Don haka da zarar na huta, zan koma, in ci gaba da aikina na taimaka wa jama’a.