Zan magance matsalar PDP-Gbenga Daniel
Tsohon gwamnan Jihar Ogun Injiniya Gbenga Daniel ya ce idan ya zama shugaban jam’iyyar PDP ta kasa, zai kawo karshen matsalar da ta dabaibaye jam’iyyar. Gbenga Daniel ya bayyana haka ne a lokacin da jirgin yakin neman zabensa ya isa Jihar Gombe, inda ya gana da shugabannin jam’iyyar PDP da kwamitin Dattawa Gbenga Daniel, da […]

Tsohon gwamnan Jihar Ogun Injiniya Gbenga Daniel ya ce idan ya zama shugaban jam’iyyar PDP ta kasa, zai kawo karshen matsalar da ta dabaibaye jam’iyyar.
Gbenga Daniel ya bayyana haka ne a lokacin da jirgin yakin neman zabensa ya isa Jihar Gombe, inda ya gana da shugabannin jam’iyyar PDP da kwamitin Dattawa
Gbenga Daniel, da yake jawabi a sakatariyar jamiyyar ta jihar, ya nuna farin cikinsa na yadda shugabannin jam’iyyar suka tarbe shi suka kuma karrama shi.
Ya ce saboda sanin darajar ‘yan Arewa ne yasa ya somo yakin neman zaben nasa daga Arewa maso Gabas inda ya sauka Jihar Gombe kana daga nan ya zaga sauran jihohin shida na shiyar.
Yace wannan zuwan nasa Gombe ba shi ne na farko ba ya zo Gombe yafi sau hudu dan tun yana Gwamna yake zuwa kuma duk zuwan da ya yi ana masa kara.
" Nazo Gombe ne dan nasan jihar PDP ce kuma jiha ce wacce duk yadda akayi ta fama da guguwar canji ta gagara inji shi
Da yake maraba da bakon shugaban jam’iyyar PDP na jihar Gombe Barista Joel Adamu Jagafa, cewa ya yi suna tare dari bisa dari da Gbenga Daniel, a jihar Gombe.
Barista Jagafa, yace ba za su ce komai ba sai dai kawai Allah ya kai mu ranar 9-10 ga watan Disamba a filin zabe inda za su nuna masa halacci na zabar sa ya zama musu jagorar jam’iyyar na kasa.
Hoto shugaban jam’iyyar PDP tare da Gbenga Danie