‘Zan magance matsalar ruwan sha a yankunan karkarar Fika’
Ta bayyana hakan ne a yayin wani rangadin gani da ido da ta kai garuruwan Janga da Boza.
Sabuwar zababbiyar Shugabar Karamar Hukumar Fika a jihar Yobe, Hajiya Halima Joda Kyari Alkamar Gudi, ta sha alwashin magance matsalar karancin ruwan sha a yankunan karkara dake yankin.
Ta bayyana hakan ne a yayin wani rangadin gani da ido da ta kai garuruwan Janga da Boza da suke fama da matsalar tsaftataccen ruwan sha.
- Kofin FA: Karo da Guardiola ba dadi – Kocin Chelsea
- ‘Ana yi wa ’yan Arewa kisan dauki dai-dai a Imo’
Ta ce garuruwan sun jima suna fama da matsalar inda kafin ta bar garuruwan ta dauki alkawarin cewa za ta yi dukkan mai yuwuwa don shawo kan matsalar.
Wasu jama’ar garin sun bayyana jin dadin su kan ziyara ta Shugabar sannan suka yi mata addu’ar fatan alkhairi da kuma yaba mata a matsayin mace shugaba abar koyi.