Zan martaba dan Adam idan na zama Gwamna – Mikati

Alhaji Shu’aibu Idris wanda aka fi sani da Mikati, ya sha alwashin cewa idan ya zama Gwamnan Jihar Kaduna zai nuna kyakkyawan shugabancin siyasa wajen ciyar da jihar gaba ta hanyoyi da dama cikin lumana ba tare da cin zarafin kowa ba. Ya bayyana haka ne jim kadan da sayen  fom tsayawa takarar Gwamna a […]

Zan martaba dan Adam idan na zama Gwamna – Mikati
Zan martaba dan Adam idan na zama Gwamna – Mikati

Alhaji Shu’aibu Idris wanda aka fi sani da Mikati, ya sha alwashin cewa idan ya zama Gwamnan Jihar Kaduna zai nuna kyakkyawan shugabancin siyasa wajen ciyar da jihar gaba ta hanyoyi da dama cikin lumana ba tare da cin zarafin kowa ba.

Ya bayyana haka ne jim kadan da sayen  fom tsayawa takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar PDP, inda ya ce ya san bukatun mutanen kauyuka da biranen jihar, “Na yi aiki da gwagwarmaya, inda ta sa na san mutum a matsayin halitta mai daraja, ba abin wulakantawa ba, kamar yadda wadansu ke yi bayan an zabe su, sun hau gadon mulki,” inji shi.

Ya kara da cewa, zai samar da tsarin bunkasa tattalin arziki da inganta ababen jin dadin rayuwa da kyautata zaman lafiya da daraja hakkin dan Adam da samar wa jama’a aikin yi da kula da kudin jihar. Sai ya kudiri niyyar jin ra’ayin jama’a kafin aiwatar da manyan ayyuka.

“Na yi takara har sau biyu a baya domin neman zama Gwamnan Jihar Kaduna, kuma ina jin dadin yadda jama’a a yanzu suka fara fahimtar mulkin farar hula da wayewar siyasar yin mutum ba jam’iyya ba,” inji shi.

 

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa