Zan mayar da Gombe sabuwar Jiha idan na ci zabe – Dan takarar Gwamna a NNPP
Dan takarar ya bayyana haka ne lokacin yakin neman zabensa a Billiri
Dan takarar Gwamnan Jihar Gombe a karkashin jam’iyyar NNPP, Khamisu Ahmed Mailantarki, ya lashi takobin mayar da Gombe sabuwar Jiha muddin aka zabe shi.
Mailantarki, wanda tsohon dan Majalisar Wakilai ne da ya wakilci mazabar Gombe da Kwami da Funakaye, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kaddamar da yakin neman zabensa na a garin Billiri.
- An dauke wutar lantarki a duk fadin kasar Pakistan
- NDLEA ta kama makaho da kuturu dauke da Tabar Wiwi
Dan takarar ya ce ba zai bai wa jama’ar Jihar kunya ba.
Mailantarki ya kuma ce idan ya ci zabe, gwamnatinsa za ta mayar da hankali sosai a bangaren ilimi kuma zai sanya dokar ta-baci don ganin duk wani dan Jihar Gombe ya samu ilimi mai nagarta.
Dan takarar, ya kuma yi alkawarin biyan kudaden jarrabawar WAEC da NECO da JAMB har zuwa karshen wa’adinsa na mulki a matsayin Gwamna.
Sannan ya yi kira ga dukkan ’yan jam’iyyar ta NNPP da cewa su fito su karbi katin zabensu domin zabar yan takarar jam’iyyar a dukkan matakai, domin babu dan NNPP da zai bai wa Najeriya kunya muddin yaci zabe a 2023.
A nasa jawabi Shugaban jam’iyyar na Jihar, Maikano Abdullahi Umar, gode wa dan takarar ya yi na yadda ya ware Naira miliyan 228 da zai raba a dukkan mazabu guda 114 da ake da su a fadin jihar a lokacin yakin neman zabensa.
Ya ce a kowacce mazaba, Mailantarki zai ba da naira miliyan biyu da babur guda daya.
Shugaban ya kuma ce duba da irin jiga-jigan da suke ficewa daga jam’iyyun APC da PDP suna komawa NNPP, hakan matakin samun nasara ne ga jam’iyyar a zaben na 2023.