Zan mika kaina ga EFCC- Fayose

Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose ya ce zai mika kansa da kansa zuwa wajen Hukumar EFCC bayan ya sauka daga mulki. A wata takarda da ya aika wa hukumar, wadda kuma ya wallafa a shafinsa na tiwita, ya bayyana wa hukumar cewa, da ya sauka a mulki, zai mika musu kansa domin amsa tambayoyin da […]

Zan mika kaina ga EFCC- Fayose
Zan mika kaina ga EFCC- Fayose

Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose ya ce zai mika kansa da kansa zuwa wajen Hukumar EFCC bayan ya sauka daga mulki.

A wata takarda da ya aika wa hukumar, wadda kuma ya wallafa a shafinsa na tiwita, ya bayyana wa hukumar cewa, da ya sauka a mulki, zai mika musu kansa domin amsa tambayoyin da suke neman amsa a gare shi.

Ayodele Fayose dai zai sauka a mulki ne a ranar 15 ga watan Oktoba, kuma ya nuna cewa a shirye yake ya mika kansa daga wannan lokacin, domin a cewarsa ya san tun tuni hukumar take neman wasu amsoshi daga gare shi, sai dai kawai saboda yana kan karagar mulki, dokar kasa ta ba shi kariya, amma daga ya sauka, shi ken an bai da wannan kariyar.  

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa