Zan rantse da Alƙur’ani ban saci kuɗin Kaduna ba — El-Rufai

Sai dai kuma ya ƙalubalanci tsofaffin gwamnonin jihar kan su rantse ba su saci kuɗin al’umma ba.

Zan rantse da Alƙur’ani ban saci kuɗin Kaduna ba — El-Rufai

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce ya shiga siyasa ne domin ya yi wa al’umma hidima, ba don ya saci kuɗi ko tara wa kansa dukiya ba.

Ya bayyana haka ne a yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Hausa na gidan rediyon Freedom da ke Kaduna.

El-Rufai, ya ce tun kafin ya zama gwamna, yana da rufin asirin da ishe sa yin rayuwa.

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, ta zargi gwamnatinsa da karkatar da sama da Naira biliyan 423 a cikin shekaru takwas da ya yi mulki, amma El-Rufai da hadiminsa sun musanta wannan zargi.

Sun bayyana cewa ana matsa wa rayuwarsu ba bisa ƙa’ida ba, wanda hakan ya samo asali daga majalisar da gwamnatin jihar.

El-Rufai ya ce ya shirya yin rantsuwa da Alƙur’ani domin ya tabbatarwa da duniya cewar bai saci kuɗin gwamnati ba.

Kuma ya ƙalubalanci sauran tsofaffin gwamnoni da shugabanni na yanzu su yi rantsuwa cewar ba su saci kuɗin al’umma ba.

Ya ce, “A kullum ina neman taimakon Allah a kan duk abin da nake yi, kuma ban taɓa niyyar cin amanar jama’ar da suka yarda da ni ba.

“Idan shugabannin Kaduna na baya za su rantse cewa ba su taɓa satar kuɗin mutane ba, ni ma zan rantse saboda ban shiga siyasa domin tara wa kaina kuɗi ba. Abin da nake da shi tun kafin na zama gwamna ya ishe ni, amma duk da haka ana zarginmu da satar kuɗi ba tare da nuna inda kuɗin suka tafi ba.”

El-Rufai ya kuma bayyana cewa an fara binciken abokansa ta hannun ICPC da EFCC d nufin ɓata musu suna.

 

Amma ya ce ya yi sallah raka’a biyu a daren ranar Juma’a tare da kai kukansa ga Allah kan wannan lamari.

Ya ce yana ci gaba da ɗaukar matakan doka, amma a yanzu ya mayar da hankali kan karatunsa da sauran harkokinsa na yau da kullum.

Ya jaddada cewa manufarsa ita ce hidimta wa al’umma, ba neman arziƙi ba.

Ya kuma ce yana da shirin dawowa siyasa a shekarar 2027, domin ba a yin ritaya a siyasa kamar yadda ake yi a aikin gwamnati.

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira