Zan rungumi duk kungiyar da ke son cigaban Arewa – Shugaban Dattawan Arewa

Sabon shugaban kungiyar Dattawa Arewa wato Arewa Elders Forum, Farfesa Ango Abdullahi ya yi alkawarin rugumar duk wata kungiya da aka kafa da manufar cigaban Arewa. Farfesan ya yi wannan bayani ne a tattaunawar da ya yi da Aminiya a Zariya. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Aminiya: Ranka ya dade yaya aka yi ka zama […]

Zan rungumi duk kungiyar da ke son cigaban Arewa – Shugaban Dattawan Arewa

Sabon shugaban kungiyar Dattawa Arewa wato Arewa Elders Forum, Farfesa Ango Abdullahi ya yi alkawarin rugumar duk wata kungiya da aka kafa da manufar cigaban Arewa. Farfesan ya yi wannan bayani ne a tattaunawar da ya yi da Aminiya a Zariya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Ranka ya dade yaya aka yi ka zama shugaba kungiyar Dattawan Arewa?

Farfesa Ango Abdullahi: Ai iyakan karin bayani ke nan cewa an taru an yi shawarar cewa ni ne yanzu zan jagoranci wannan kungiya. Ban nema ba, wadanda suka ga abin ya dace a yi a haka su suka dauki wannan mataki. Iyaka abin da na ce musu kawai shi ne na gode, da kuma fatan Allah Ya taimakemu sauke nauyin da aka dora mani ya zama zan iya dauka tare da gudumuwarsu. 

Aminiya: Kasancewar ka zo a ciki a lokacin da Arewa ke cikin tsaka mai wuya musamman fadan kabilanci, da na addini. Wane irin mataki kake shirin dauka ganin cewa ka kwantar da hankkalin jama’ar Arewa baki daya?

Farfesa Ango Abdullahi: To dama ai kullum a cikin haka ake. A shekarun nan a Arewan ta samu kungiyuyi da dama, kuma kusan duk manufufin iri daya ne, akwai bambanci a wasu wurare, amma kusan idan ka dube su duka za ka ga cewa suna ikirarin cewa za su dauki matakai ne wadanda za su tabbatar da cewa sun kwato hakkokin Arewa ta kowace fuska a cikin zamantakewar da ake yi a wannan kasa, saboda haka ni abin da zan kara shi ne kawai nauyin da yake kaina shi ne wannan kungiyoyi mu jawo su kusa mu hada su wuri guda kamar yadda na fara. Mako biyu da suka wuce an sami zama da kungiyoyi goma sha takwas a garin Kaduna, kuma bayan zaman da aka yi ne aka bayar da wata sanarwa wanda za a ce ta yi wa wadansu dadi, amma kuma kila ba ta yi wa wadansu dadi ba, amma dai sanarwa ce wadda ta fito daga kungiyoyi 18, kuma a haka za mu ci gaba kungiyoyi da a da ba su a cikin irin wannan taro, suma za a jawo su suma su zo mu ji nasu ra’ayi, domin jin ra’ayin shi ne zai samar da ra’ayin mutanan Arewa gaba daya.

Aminiya: Mutane suna muku ganin kamar siyasa na shiga cikin harkokinku, me za ka ce game da wannan batu?

Farfesa Ango Abdullahi: To ai dama mun kafa wannan kungiyar saboda siyassa ne, sai dai ba mu ce muna da jam’iyya ba, amma duk abubuwan da suka shafi mutanan kasar nan ai suna da alaka da siyasa, saboda haka muna nan a kan matakin cewa idan muka ga wasu abubuwa wadanda aka yi wadanda muka gamsu da su cewa sun yi wa Arewa daidai, za mu yi yabo, inda kuma wadannan abubuwa  suka saba wa  jin dadin  jama’ar Arewa wannan kuma sai mu tsawatar, ko kuma mu yi fada a kai. Wannan kuma a haka muke har yanzu.

Aminiya: Kwanakin baya kun ce Shugaba Buhari dan Arewa ne kuma gashi bai wa Arewan komai ba, har yanzu kuna nan akan bakanku?

Farfesa Ango Abdullahi: To wannan taro da muka gudanar a Kaduna wanda na fada maka cewa kungiyoyi goma sha takwas sun taru a mako biyu da suka gabata, matsayin da suka nuna ke nan a cikin shawarwarin da aka yi  a ranar na cewa ba mu gamsu da wannan mulkin ba domin ba abin da aka yi wa Arewa, to saboda haka bani da iko in juya abin da wannan taro ya ce, kuma  na yarda da abin da taron ya ce domin ba taro na bane ni kadai, taron kungiyoyi ne har goma sha takwas kuma shawarwarin da suka yanke ke nan, kuma dole ne kowa ya zauna a kan wannan shawaran.

Aminiya: Kwanan nan ne aka fitar da sunayen wadanda suka wawure kudaden Najeriya ko me za ka ce game da wannan?

Farfesa Ango Abdullahi: Da sunanka a ciki ne? tunda ba sunanka sai kawai ka sa gilashi ka sake karanta sunayen wadanda aka rubuta. Ai kawai ni wadanda na gani na karanta sai kawai na ga kamar ai idan dai su kadai ne suka kwashi ganima a Najeriya, to ai bai kamata a ce Najeriya ta tsiyace haka ba.

Kuma yanzu to da ni ne shugaba bai kamata in rika magana barkatai haka ba, muna da tsare-tsaren yadda za a rika gudanar da komai na kungiyar, kuma mun zabi wanda zai rika magana da yawun kungiya kuma wanda muka zaba shi ne Dokta Hakeem Baba Ahmed, za mu bayyana sunayan duk masu rike da mukamai a wannan makon da muke ciki. Don haka ina kira ga duk wani mai kishin Arewa da ya sa natsuwa tare da kokarin kawo wa Arewa duk wani cigaba mai amfani.