Zan samar da wutar lantarki a Najeriya -Jonathan
Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya ce gwamnatinsa ba za ta huta ba har sai ta samar da wutar lantarki a kasa baki daya. Ya yi alkawarin ne yayin da yake kaddamar da tashar samar da wutar lantarki a jihar Legas wacce za ta samar da wuta mai karfin megawatt 220.Ya ce ‘A bangaren gwamnati […]
Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya ce gwamnatinsa ba za ta huta ba har sai ta samar da wutar lantarki a kasa baki daya.
Ya yi alkawarin ne yayin da yake kaddamar da tashar samar da wutar lantarki a jihar Legas wacce za ta samar da wuta mai karfin megawatt 220.
Ya ce ‘A bangaren gwamnati ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai mun tabbatar wutar lantarki ta samu a kasa baki daya’.
Ya ci gaba da cewa gyaran da gwamnati ta yi wa tashar wutar lantarkin ta sanya tashar ta dawo cikin hayyacinta inda take samar da megawat dubu daya da dari uku da ashirin.
Ya bayyana cewa nasarar da aka samu ita ce ta farko tun lokacin da aka kafa tashar wutar lantarkin.
Ya ce karfin wutar da tashar za ta rika samarwa zai taimakawa kamfanonin da ke jihar Legas da kewaye tare da samar da ayyukan yi a jihar.
Shugaban kasar ya kara da cewa tsare-tsaren da gwamnatinsa take da shi kan wutar lantarki zai taimaka wajen kawar da duk wani kalubale da ke fuskantar bangaren wutar lantarki a Najeriya.
A cewarsa sayar da kamfanonin wutar lantarkin da gwamnatinsa ta yi ga kamfanoni masu zaman kansu ya samar da riba mai yawa ga Najeriya.