Zan sayar da kamfanin NNPC idan aka zabe ni – Atiku

Dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa idan ya zama shugaban kasar Najeriya zai saida kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC. Atiku ya bayyana hakan ne a wani taro da ya yi da ‘yan kasuwa a jihar Legas a jiya Laraba. Atiku ya ce, ya taba yunkurin baiwa […]

Zan sayar da kamfanin NNPC idan aka zabe ni – Atiku

Dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa idan ya zama shugaban kasar Najeriya zai saida kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC.

Atiku ya bayyana hakan ne a wani taro da ya yi da ‘yan kasuwa a jihar Legas a jiya Laraba.

Atiku ya ce, ya taba yunkurin baiwa tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo shawarar sayar da kamfanin NNPC amma shugaban bai rattaba hannun amincewar hakan ba.

Tsohon Mataimakin shugaban kasar ya ce “Zan tabbatar da sayar da NNPC ko da za su kashe ni.”

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta