Zan sayi kulob din Arsenal ne don daukaka martabar Najeriya -Aliko dangote
Shahararren attajiri dan Najeriya Alhaji Aliko dangote ya bayyana dalilinsa na son ya saye kulob din Arsenal da ke Ingila maimakon ya sayi wani kulob a Najeriya. A lokacin da yake hira da manema labarai a karshen makon jiya, ya ce dalilin da yake son ya saye kulob din Arsenal sun hada da kokarin yada […]
Shahararren attajiri dan Najeriya Alhaji Aliko dangote ya bayyana dalilinsa na son ya saye kulob din Arsenal da ke Ingila maimakon ya sayi wani kulob a Najeriya.
A lokacin da yake hira da manema labarai a karshen makon jiya, ya ce dalilin da yake son ya saye kulob din Arsenal sun hada da kokarin yada sunan Najeriya a idon duniya, inda ya ce idan ya samu nasarar yin haka babu shakka sunan Najeriya zai dada daukaka a idon duniya, don haka duk wanda ya tambaya za a ce masa dan Najeriya ne ya mallaki kulob din kuma yin haka ba karamar nasara ce a gare shi da daukacin Najueriya ba.
Ya bayar da misali da Roman Abramobich, attajiri dan asalin Rasha wanda yanzu haka shi ya mallaki kulob din Chelsea da ke Ingila. Ya ce a duk lokacin da aka ambaci sunan Roman Abramobich a matsayin wanda ya mallaki kulob din Chelsea, babu abin da ke zuwa zukatan mutane sai dan asalin Rasha ne. “”Ka ga da zarar an ambaci sunansa babu abin da ke zuwa zukatan mutane illa daga kasar Rasha yake, don haka nake so na yi koyi da shi don daukaka martabar Najeriya”.
A kwanakin baya ne jama’a da dama suka rika caccakar Aliko dangote a kan yunkurinsa na saye kulob din Arsenal alhali ya kasa sayan wani kulob a gida irin su Kano Pillars da El-Kanemi Warriors da sauransu. Wasu kuma suka ce idan ma ba zai sayi wani kulob a gida ba, to ya kafa nasa don bunkasa harkar kwallo a Najeriya. Hakan ce ta sa attajirin ya fito karara ya bayyana dalilin da ya sa yake so ya mallaki Arsenal.