Zan shiga tsakani don sasantawa da ’yan Boko Haram – Gowon
Tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ya bayyana kudirinsa na shiga tsakani domin sasantawa tsakanin gwamnati da ’yan Boko Haram idan aka ba shi goyon baya don kawo karshen kashe-kashe da lalata dukiyar jama’a a yankin Arewa maso Gabas.Janar Yakubu Gowon ya bayyana haka ne a garin Gombe lokacin da ya halarci wani taro da […]
Tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ya bayyana kudirinsa na shiga tsakani domin sasantawa tsakanin gwamnati da ’yan Boko Haram idan aka ba shi goyon baya don kawo karshen kashe-kashe da lalata dukiyar jama’a a yankin Arewa maso Gabas.
Janar Yakubu Gowon ya bayyana haka ne a garin Gombe lokacin da ya halarci wani taro da Hukumar kaya kasashe ta Majalisar dinkin Duniya (UNDP) ta shirya da hadin gwiwar hukumomin domin nemo mafita kan tabarbarewar tsaro da yankin Arewa maso Gabas ya shiga.
Janar Gowon ya kuma ce kamar yadda jama’ar da ke wannan dakin taro suka ji Shehun Borno ta bakin wakilinsa Dokta Musa Liman ya fada wa jama’a cewa wannan kungiya ta Boko Haram ba kungiyar Musulmi ba ce sun ari rigar Musulunci ne suna bata wa Musulmi suna, ya ce shi ma a saninsa Musuluncin da ya sani da wanda kowa ya sani yana koyar da zaman lafiya ne.
Daga nan sai Janar Gowon ya yi kira ga ’yan kungiyar Boko Haram su yi wa Allah su daina kashe- kashen idan kuma suna so ne a zauna da su don a tattauna matsalolin da ke faruwa a shirye yake ya ba da tasa gudunmawar kuma a ko’ina suke son a zauna a fadin
duniyar nan ya shirya wa haka.
Ya ce ba sai lallai a boye ba koda a bayyane ne suke son a yi zaman ko a kasar Chadi ne zai so a zauna da su, kuma ya ce ya fadi haka ne ta hannun ’yan jarida saboda ya
tabbata suna jin sa.
Janar Gowon ya ce zai ba da kansa ne don shiga tsakanin saboda kishin kasarsa don ganin an zauna an tattauna don samo mafita a ceto al’ummar da wannan bala’i ta fi shafa a yankin Arewa maso Gabas domin zaman lafiyar da aka rasa ya sake dawowa.