Zan so na koyi yadda Ahmed Lawan zai koma majalisa ba tare da takara ba — Okorocha
Ba na jin akwai wani abu mai sarkakiya a ciki da har sai an koya maka.
Sanata Rochas Okorocha ya yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan shagube kan yadda zai koma zauren Majalisar Tarayya ta 10 ba tare da ya fita an fafata da shi a zaben fidda gwani ba.
Tsohon gwamnan na Jihar Imo ya ce har yanzu yana mamakin yadda aka yi Sanata Lawan wanda ya yi takarar kujerar Shugaban Kasa ya samu damar komawa Majalisar Dattawa.
- Osimhen: Mai tallan burodi da ya zama dan kwallo mafi daraja a Afirka
- Dalilin da aka kai samame gidan Matawalle — Gwamnatin Zamfara
A bisa wannan dalili ne Sanata Okorocha ya ce zai zo ya dauki darasin irin wannan cakwakwiyar a wajen Shugaban Majalisar Dattawan mai barin gado.
Sanata mai wakiltan Imo ta Yamma, Rochas Okorocha, ya bukaci Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da ya koya masa yadda ake komawa majalisar dattawan ba tare da mutum ya yi takara a zaben fidda gwani ba.
Okorocha ya fadi hakan ne yayin zaman bankwana na Majalisar Dattawa ta 9 da aka gudanar a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni.
A halin yanzu dai Sanata Lawan zai kasance cikin mambobin Majalisar Dattawa ta 10 da za a rantsar a makon gobe, duk da cewa ya yi yunkurin zama dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC.
Ana iya tuna cewa, Sanata Lawan da Okorocha sun yi takara a zaben fidda gwani na neman tikitin jam’iyyar APC, amma suka sha kaye a hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A bisa ka’ida, shiga zaben fidda gwanin neman takarar Shugaban Kasa da Sanata Lawan ya yi zai hana shi neman tikitin kujerar sanata mai wakiltan Yobe ta Arewa a jam’iyyar APC, kamar yadda Dokar Zabe ta tanadar.
A kan haka ne aka ayyana Bashir Machina a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin takarar kujerar Sanatan Yobe ta Arewa na jam’iyyar APC, wanda kuma Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta tabbatar da shi.
Sai dai kuma daga bisani labari ya sha banban, inda hukuncin Kotun Koli ya tabbatar da Sanata Lawan a matsayin dan takarar wannan kujera na hakika duk da cewa bai shiga an fafata da shi ba.
Da yake jawabinsa a zaman na bankwana, Rochas ya ce, “zan zo ka [Sanata Lawan] koya mani yadda ka koma majalisa ba tare da takara a zaben fidda gwani ba.
“Da ni da kai duk ba mu yi takarar kujerar Majalisar Dattawa ba a wannan karon. Kawai takarar kujerar shugaban kasa na yi. Amma sai ta kasance kai dan siyasa ne mai wayo.
“Yadda aka yi ka koma Majalisar Dattawa wani shafi ne a tarihin siyasarmu wanda akwai bukatar mu yi nazari a kansa.
“Na kasance a filin daga tare da kai muna neman shugabancin kasa, na rasa yadda aka yi ka samu nasarar yi mana zagon kasa har ga shi za ka dawo ka bar wasunmu.
“Nan gaba akwai bukatar ka koya mun yadda ka aka yi ka aikata wannan dabara.”
Lawan ya mayar wa Okorocha da martani
A martaninsa, Lawal ya ce: “Abu ne mai sauki. Na kasance tare da kai a filin daga kuma bayan mun sha kasa, mazabata ta ce sun sake nazari don haka suna bukata na.
“Su suka nemi na dawo kuma tafiya ce mai wahala don sai da lamari ya kai har gaban kotu.
“Ban ma daukaka kara kan hukuncin da ya hana ni takara ba. Jam’iyyarmu [APC] da sauran masu ruwa da tsaki ne suka daukaka kara a madadina har zuwa Kotun Koli, don haka babu wani babban abu.
“A zahirin gaskiya ba, ba na jin akwai wani abu mai sarkakiya a ciki da har sai an koya maka.