Zan so sirikina ya zama gwamna idan na kammala wa’adina- Gwamnan Imo

Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha ya ce mijin ‘yarsa Uche Nwosu ne yake so ya ci gaba da mulkin jihar bayan ya kammala wa’adinsa a shekarar 2019. Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan Jam’iyyar APC na cikin garin Owerri a gidan gwamnatin jihar. Shi dai Nwosu a yanzu […]

Zan so sirikina ya zama gwamna idan na kammala wa’adina- Gwamnan Imo

Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha ya ce mijin ‘yarsa Uche Nwosu ne yake so ya ci gaba da mulkin jihar bayan ya kammala wa’adinsa a shekarar 2019.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan Jam’iyyar APC na cikin garin Owerri a gidan gwamnatin jihar.

Shi dai Nwosu a yanzu shi ne shugaban ma’aikatan gidan gwamnati na jihar.

“Shugaban ma’aikata bai fada min cewa zai tsaya takarar gwamna ba. Amma idan har fito to ina tare da shi.

“Nwosu mutum mai kwazo kuma bay a gajiya. Mutum ne mai Kankan da kai kuma matashi dab a ya jijji da kai.”