Zan soke shirin kyautata zaman yara da aka shigo da su Amurka – Trump

SHugaban Amurka Donald Trump ya ce zai soke shirin nan da ake kira da Ingilishi Deferred Action For Children Arribal, (DACA) da tsohon Shugaban Amurka Barrack Obama ya samar da niyyar taimaka wa yara ’yan kasashen waje musamman kasashe da ke makwabtaka ta Amurka irin su Meziko don ba su damar  zama Amurkawa tare da […]

Zan soke shirin kyautata zaman yara da aka shigo da su Amurka – Trump

SHugaban Amurka Donald Trump ya ce zai soke shirin nan da ake kira da Ingilishi Deferred Action For Children Arribal, (DACA) da tsohon Shugaban Amurka Barrack Obama ya samar da niyyar taimaka wa yara ’yan kasashen waje musamman kasashe da ke makwabtaka ta Amurka irin su Meziko don ba su damar  zama Amurkawa tare da tallafa musu domin su zauna cikin kasarsu kuma yi rayuwa kamar ko wani dan kasa.

Shirin yana bai wa yaran damar samun duk wata dama da wani dan asalin Amurka zai samu. Kuma Shugaba Obama ya samar da shirin ne, duk da cewa an tabbatar da cewa ana shigo da yaran zuwa Amurka ta barauniyar hanya, amma ya yi musu afuwa kuma ya ba su dama ta musammam domin su gudanar da rayuwarsu.

Tun daga wancan lokaci ne aka tantance su kuma aka ba su takardar da shaida cewa Gwamnatin Amurka ta san da zamansu.

To sai dai kuma, tun daga wancan lokacin da yawan iyaye daga kasashe makwabta suka fara amfani da wannan dama suna tunkudo ’ya’yansu ba tare da iyayen sun biyo su ba domin samun wannnan garabasa. Da yawansu gwamnati ta kyale su kuma ta bar iyayensu suka biyo su daga baya.

To sai dai zuwan Shugaba Donald Trump ya yi yunkurin soke wannan kyautatawa da ake wa yaran inda ya ce gwamnati na kashe kudi mai yawa, sai dai yunkuri nasa ya ci karo da suka daga ’yan Jam’iyyar Democrat da ma ’yan jam’iyyarsa ta Republican.

Da yawansu sun ce yaushe za a kori yaran da suka shigo Amurka ba da saninsu ba, bayan sun yi nisa da rayuwarsu.Wannan ya sa tilas aka sa kaso na musammam a cikin kasafin kudi da aka saba kebewa domin yaran, kuma hakan bai yi wa Shugaban dadi ba.

Kuma bayan jingine wannan batu, a farkon watan nan Shugaba Trump ya ba da umarnin dakatar da wannan shiri na taimakon wadannan yara.

Ya ba da umarnin cewa a sanya tsauraran matakan tsaron shige da fice a Amurka musamman kasashe masu shigowa da yaransu domin samun cin gajiyar shirin DACA.

Trump ya bai wa jami’an shige-da-fice da ke aiki a bakin iyakar Amurka musamman  kasashen da ke shigowa Amurka da yaransu domin su amfana da wannan shirin umarnin su sanya ido sosai. Ya ce dokokin da aka sa da na a kama a sake ya sa masu shigowar ba su mayar da dokar shigowa Amurka bakin komai ba, don haka daga yanzu duk wanda aka kama ya shigo ba da izini ba, musammam masu shigowa ayari-ayari da niyyar amfana da shirin DACA, a tabbatar an gurfanar da su a gaban kotu, tare da yi musu hukuncin shigowa Amurka ba bisa ka’ida ba.

Gwamnatin Trump ta kawo karshen shirin a cikin watan Satumba, amma kuma ta ba majalisar kasar dama su fito da tsari na dindindin a kan makomar masu amfana da shirin.

Tun da farko Trump ya ce zai amince da ci gaban shirin DACA ne, matukar majalisun kasar sun tabbatar da kudaden da za a aiwatar da gina katanga a kan iyakar Kudancin kasar da Meziko. 

Shugaban na Amurka ya soki lamirin kasar Meziko cewa ba ta yin komai game da hana mutanenta kwarara cikin Amurka musammam yara da niyyar cin gajiyar shirin na DACA.

An dai ware kudi  Dala tiriliyan daya da kusan rabi a cikin kasafin kudin bana wanda kuma an ware wa shirin na DACA rabo mai tsoka, sai dai an yi haka ne ba da son Shugaban na Amurka ba.

To sai dai duk da wannan matakin da Trump ya dauka yanzu, ’ya’yan Jam’iyyar Democrat a Majalisar Wakilai sun bukaci takwarorinsu na Republican da a samar da matsaya a kan wannan batu ta hanyar kuri’a.

A waje daya kuma, alkalan manyan kotunan Amurka sun bukaci Gwamnatin Tarayyar Amurka ta aiwatar da wasu daga cikin yarjejeniyar da aka yi game da wannan shiri na DACA, wasu kuma su bari sai abin da dokar kasa ta ga ya dace a yi.