Zan tabbatar APC ta ƙwace Kano a 2027 – Doguwa

Doguwa ya ce zai bai wa ‘yan adawa a Kano mamaki a zaɓen 2027.

Zan tabbatar APC ta ƙwace Kano a 2027 – Doguwa

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Doguwa/Tudun-Wada a Jihar Kano, Alhassan Ado Doguwa, ya lashi takobin kawo wa jami’yyar APC nasara a zaɓen 2027 a jihar.

Doguwa, ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Lahadi, yayin da yake mayar wa Abdulmumini Jibrin Kofa na jami’yyar NNPP martani, biyo bayan cece-kucen da ya ɓarke a tsakaninsu.

Kofa, ya ce Doguwa ba komai ba ne a jami’yyar APC face matsala.

Sai dai Doguwa, ya ce zai tabbatar da samun nasarar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

Ya ƙara da cewar akwai buƙatar a ba shi muƙamin Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a 2027 don bai wa mara ɗa kunya.

“Ina so na yi amfani da wannan dama domin na nuna girmamawa ga shugabannin jam’iyyarmu da su ba ni muƙamin Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen Jihar Kano a 2027.

“Ni ba matsala ba ne siyasa a Kano; ni dukiya ne, abin alfahari ga jam’iyyar APC a jiha da kuma matakin ƙasa,” in ji shi.

Idan ba a manta ba, Doguwa ne kaɗai ɗan majalisa da aka zaɓa a jam’iyyar APC a zaɓen 2023 a yankin Kano ta Kudu.

Doguwa na wakiltar mazaɓar Tudun-Wada/Doguwa a Majalisar Tarayya, kuma shi ne shugaban kwamitin majalisa kan albarkatun man fetur.

A baya-bayan nan dai, Doguwa da Kofa sun dinga musayar yawu a kafafen watsa labarai.

Kofa ya zargi Doguwa da kawo cikas ga zaman lafiya a Jihar Kano.

Dambaruwar tsakanin ’yan siyasar na Kano, ya samo asali ne bayan da Doguwa ya caccaki jagoran NNPP na ƙasa Rabiu Musa Kwankwaso.

Kofa ya yi martani ne don kare martabar Kwankwaso daga jami’yyar adawa ta APC a jihar.

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS

Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar rushe Hukumar EFCC