Zan tilasta sanya ‘ya’yanmu a makarantun gwamnati – Masari

dan takarar gwamnan Jihar Katsina kuma tsohon Shugaban Majalisar Wakiliai Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana dan takarar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari a matsayin maganin matsalolin da suka addabi kasar nan, inda ya bukaci al’ummar kasar nan su mara masa baya. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Wane kira kake […]

Zan tilasta sanya ‘ya’yanmu a makarantun gwamnati – Masari
Zan tilasta sanya ‘ya’yanmu a makarantun gwamnati – Masari

dan takarar gwamnan Jihar Katsina kuma tsohon Shugaban Majalisar Wakiliai Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana dan takarar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari a matsayin maganin matsalolin da suka addabi kasar nan, inda ya bukaci al’ummar kasar nan su mara masa baya. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Wane kira kake da shi ga ’yan Najeriya musamman ganin zabukan da ke tafe?
Masari: Da farko mun kawo ziyara Jihar Kaduna ne saboda taro da ’Yan kungiyar Katsinawa da Daurawa mazauna jihar.  Game da tambayar da ka yi mini kuma, akwai bukatar mutanen kasar nan su zabe Janar Buhari a zabe mai zuwa domin dukkanmu mun san ya cancanta. Gaskiya wannan ita ce damarmu ta karshe da zamu iya taimaka masa ya zama shugaban kasar nan domin idan har wannan dama ta kubuce mana, to zamu zama abin tausayi a kasar nan.  Kamar kuma aka sani ina neman kuri’un Katsinawa da duka jama’a da ke jihar saboda burina na zama gwamnan jihar a zaben badi.
Aminiya: Wane albishir kake da shi ga jama’ar Jihar Katsina idan ka zama gwamna?
Masari: Idan Ubangiji ya sa na zama gwamna, ’ya’yana da iyalina makarantu da asibitin gwamnati za su rika zuwa. idan har muna san dawo da martabar makarantun mu, tilasta ne ’yayanmu da matanmu su rika halartar makarantun gwamnati da asibitocin gwamnati kamar yadda ’yayan talakawa ke zuwa. Dole ne idan har kana san shiga gwamnatinmu sai ka amince ’yayanka da matanka za su rika zuwa makarantun gwamnati da asibitocin gwamnati. Tun kafin samun mulkin kai, gwamnatin lardin Katsina ita ke samar kudin da ake kula da makarantun firamare da biyan malamai da ma’aikatan ilimi da asibitoci da malaman asibitoci, kuma ita ke kulada ‘yan sandan lardin da alkalai kuma babu banbanci tsakanin makarantun ma’aikatan gwamnati da na sauran jama’a ko cibiyoyin kula da lafiya.
Sai ga shi  yau idan aka ce ba samu kudi daga asusun tarayya ba, wata kila Jihar Katsina ta durkushe domin duk wadansu harkoki da hanyoyin da za a samu kudi an watsar da su. Noma da kiwo, wadanda su ne ginshikan rayuwar kowace al’umma, kuma shi ne jama’ar Jihar Katsina suka dogari da shi wajen rayuwasu.
Aminiya: Wadande abubuwa gwamnatinka za ta bai wa fifiko?
Masari: Daga cikin manyan abubuwan da zan baiwa fifiko akwai ilimi da kiwon lafiya da harkokin noma da sauransu domin inganta rayuwar Jihar Katsina baki daya.