Zan tsaya takara idan Buhari bai tsaya ba-Yerima

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yerima ya ce zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019 idan Shugaba Muhammadu Buhari bai tsaya ba. Yerima ya fada wa manema labarai jiya a Abuja cewa furucin da ya yi ba zai kawar da kudurinsa na goyon bayan shugaba Buhari ba idan ya yanke shawarar […]

Zan tsaya takara idan Buhari bai tsaya ba-Yerima

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yerima ya ce zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019 idan Shugaba Muhammadu Buhari bai tsaya ba.
Yerima ya fada wa manema labarai jiya a Abuja cewa furucin da ya yi ba zai kawar da kudurinsa na goyon bayan shugaba Buhari ba idan ya yanke shawarar tsayawa takara.
Yerima wanda yake wakiltar Zamfara ta Yamma a jam’iyyar APC wanda har ila yau ya goyi bayan kudurin da shugabannin jam’iyyar suke yanke na amincewa da shugaban kasa ya sake tsayawa takara a zabe mai zuwa ya ce ba zai yi takara da Buhari ba.