Zan turo wakilai da za su halarci bikin rantsar da Tinubu — Joe Biden

Tawagar ta Amurka za ta kasance karkashin jagorancin Ministar Gidaje da Raya Birane, Marcia L. Fudge.

Zan turo wakilai da za su halarci bikin rantsar da Tinubu — Joe Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce zai turo wakilan gwamnatinsa da za su halarci bikin rantsar da sabon Shugaban Najeriya Bola Tinubu.

Biden, ta wata sanarwa a shafin gwamnatin Amurka ranar Litinin, ya ce tuni sun kafa tawagar mutane tara karkashin jagorancin Sakatariyar Raya Gidaje da Birane ta Amurka, Marcia L. Fudge da za su halarci bikin rantsuwar a Abuja, babban birnin Najeriya.

Wannan sanarwar na zuwa ne kwanaki kadan bayan sukar da tsohon dan takarar Shugaban Kasa na PDP Atiku Abubakar ya yi wa kasar, bayan da Sakataren Gwamnatin Amurka, Antony Blinken, ya taya Tinubu murnar cin zabe.

Atiku ya ce sabanin matsayin da gwamnatin Amurka ta bayyana wa duniya kan zaben da ta ce tana sane da irin magudin da aka tafka, bai kamata a ce ta amince wa zaben ba wanda akasarin al’umma suka yarda yana cike da magudi.

Baya ga wakilan Shugaban Amurkan, tsoffin Shugabannin Kasashe da dama da shugabannin manyan kungiyoyin kasashen duniya da wakilansu da dama sun amsa gayyatar halartar bikin rantsuwar.

Kazalika tsohon Shugaban Kasar Kenya, Uhuru Kenyatta zai halarci bikin, inda har zai gabatar da wata mukala ranar 27 ga wata, duk dai a cikin shirye-shiryen rantsuwar.

Za a rantsar da Tinubu, tsohon gwamnan Jihar Legas a matsayin shugaban Najeriya na 16, a ranar ta 29 a dandalin Eagle Square da ke Abuja

Tun daga ranar Alhamis za a fara gudanar da bikin inda Shugaba Muhammadu Buhari mai barin-gado zai bai wa Tinubun lambar girmamawa mafi girma ta Najeriya wato GCFR wadda ake ba shugaban kasa, sai kuma mataimakinsa Kashim Shettima wanda za a ba shi lambar da ke bi mata ta GCON.