Zan yi bakin kokari na don kada Buhari a zaben 2019- Atiku

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta PDP kuma tsohon Maitaimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce zai yi iya bakin kokarinsa don kada Shugaba Buhari daga mulki, a zaben shekarar 2019. Atiku ya bayyana hakan ne a jiya Laraba wajen wani taron shugabannin kabilar Igbo a Enugu. Atiku ya ce, ko dai ya […]

Zan yi bakin kokari na don kada Buhari a zaben 2019- Atiku

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta PDP kuma tsohon Maitaimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce zai yi iya bakin kokarinsa don kada Shugaba Buhari daga mulki, a zaben shekarar 2019.

Atiku ya bayyana hakan ne a jiya Laraba wajen wani taron shugabannin kabilar Igbo a Enugu.

Atiku ya ce, ko dai ya ci zabe ko ya fadi Shugaba Buhari ba zai ci gaba da mulkin Najeriya ba.