Zan yi kokarin ganin an cire dokar hana sa dankwali a Majalisar Amurka – Ilhan Omar

Zababbar ’yar majalisar Amurka Ilhan Omar wadda tana daya daga cikin mata musulmi da suka samu nasarar lashe zabensu a zabukan rabin zango da aka gudanar a Amurka, ta bayyana shirinta na yin duk mai yiwuwa wajen ganin an cire dokar hana musulmi sanya dankwali a majalisar. Ita ma Jam’iyyar Democrats wadda ita ce ke […]

Zan yi kokarin ganin an cire dokar hana sa dankwali a Majalisar Amurka – Ilhan Omar

Ilhan Omar

Zababbar ’yar majalisar Amurka Ilhan Omar wadda tana daya daga cikin mata musulmi da suka samu nasarar lashe zabensu a zabukan rabin zango da aka gudanar a Amurka, ta bayyana shirinta na yin duk mai yiwuwa wajen ganin an cire dokar hana musulmi sanya dankwali a majalisar.

Ita ma Jam’iyyar Democrats wadda ita ce ke da rinjaye a majalisar, ta sanar da cewa za ta yi kokari wajen cire dokar.

A cewar Ilhan, “babu wanda ya sanya min dankwali a kaina. Ni na sanya wa kaina. Zabina ne, wanda kuma yana cikin tsarin kundin mulkin Amurka kamar yadda aka gyara.

Ilhan Omar dai tana sanya dankwali da karamin mayafi mai rufe kai, kuma a tsarin majalisar wanda yanzu yake da kimanin shekara 181, dole duk wani mamba a majalisar ya bude kansa, kuma ba zai ma shiga majalisar ba dole sai ya bude kansa.

Wannan kudurin dai ya fara samun armashi bayan wasu matan da suka samu nasara irinsu Nancy Pelosi da Jim McGobern.